140926-allah-1-gari-bamban-Lubabatu.m4a
|
Daga ranar 3 zuwa ranar 7 ga watan Oktoba, maniyyatan da suka fito daga sassa daban daban na duniya za su fara gudanar da aikin hajji na bana, aikin da ya kasance daya daga cikin manyan ginshikai biyar ga musulmi.
Kasar Sin kasa ce da ke da dimbin musulmi, wadanda yawansu ya kai sama da miliyan 20, kuma a fannin gudanar da aikin hajji ma ba a bar su a baya ba, don haka, tun daga ranar 5 ga wata ne suka fara tashi zuwa kasa mai tsarki don gudanar da aikin. Domin samun karin haske, sai a biyo mu cikin shirin.(Lubabatu)