141001-Tasirin-matsalar-sauyin-yanayi-ga-ci-gaban-duniya-Sanusi.m4a
|
A jawabinsa, babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon ya ce, kowa da kowa a duniya yana dandana tasirin sauyin yanayi, kamar ambaliyar ruwa, mahaukaciyar guguwa, kwararowar Hamada, fari, zaizayar kasa da sauran bala'u inda rayukan jama'a da dukiyoyi ke salwanta.
Masana na ganin cewa, lokaci ya yi da shugabanni da sauran masu ruwa da tsaki a wannan harka za su mutunta yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayi a taron da ke tafe a Paris na kasar Faransa a shekarar 2015.
Sai dai a lokacin da ake musayar ra'ayoyi kan yadda za a magance wannan matsala,kananan kasashe na zargin kasashen da suka ci gaba da rashin cika alkawuransu game da sauyin yanayi.
Yanzu dai kasar Jamus ta yi alkawarin zuba jari na dala biliyan 1 ga asusun kiyaye muhalli a shekaru hudu masu zuwa, yayin da Sin a matsayinta na kasa mai tasowa ta sanar da yin kokari tare da kasashen duniya wajen tunkarar matsalar sauyin yanayi tare da ninka gudumawar da ta bayar.
Bugu da kari Sin ta ba da shawarar kafa asusun hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa kan tunkarar sauyin yanayi.
Masu fashin baki na ganin cewa, idan har ba a magance matsalar sauyin yanayi dake barazana ga ci gaban duniya ba, hakika za ta yi mummunan tasiri ga ci gaban tattalin arziki, lafiya, zamantakewar jama'a da sauran fannoni na rayuwa har ma da ci gaban duniya baki daya. (Ibrahim/Sanusi Chen)