in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirin tashar sararin samaniya na janyo hankulan kasashen duniya
2014-09-15 17:52:09 cri

A 'yan kwanakin baya bayan nan ne aka shirya wani taron shekara-shekara karon na 27, na kungiyar masu binciken sararin samaniya a nan birnin Beijing, inda hukumar kasar Sin ta bayyana cewa, za a kammala aikin kafa tashar sararin samaniya mallakar kasar kafin shekarar 2022, wadda za ta taimaka matuka wajen samar da hidima ga Bil Adama wajen nazarin sararin samaniya.

An dai kafa kungiyar masu binciken sararin samaniya ne a shekarar 1985, kuma dukkan mambobin kungiyar sun fito ne daga 'yan sama jannati na kasashen duniya daban daban, wadanda suka taba aiwatar da ayyukan sarrafa kumbo mai daukar mutane. Kuma taron na bana shi ne karon farko da kungiyar ta gudanar a nan kasar Sin.

A yayin taron, 'yan sama jannati mahalartansa na kasa da kasa sun ziyarci cibiyar sararin samaniya dake arewacin birnin Beijing, da na'urorin da ake amfani da su wajen horo, da samfurin kumbon Tiangong-1, da kuma sauran gine-gine, inda kuma suka tattauna kan batutuwan da suka shafi yadda suke gudanar da ayyukansu game da sararin samaniya, da shirye-shiryen sararin samaniya a nan gaba, da kuma hadin kai tsakanin kasa da kasa da dai sauransu. Kana sun ziyarci wasu jami'ai, da cibiyoyin nazarin ilimin kimiya, da kamfanoni na kasar Sin, don yin cudanya da dalibai da kwararru a fannin kimiyya da dai sauransu.

A wani bahon ababe marasa nauyi dake cibiyar horar da 'yan saman jannati ta kasar Sin, wani ma'aikacin cibiyar yana bayyana wa 'yan sama jannatin da suka fito daga kasashe 19, yanayin da na'urorin ababen da ake amfani da su wajen horor da 'yan sama jannatin a kasar Sin.

Saboda sana'ar bai daya da suke dauka, wadannan 'yan saman jannatin sun nuna sha'awa sosai kan abubuwan da suka gani. Russell Schweickart, 'dan samman jannati daga kasar Amurka, wanda ya taba taba je sararin samaniya da kumbon Apollo-9 mai dauke da mutane a shekarar 1966, ya bayyana cewa,

"Ina matukar sha'awar na'urorin da ake amfani da su a nan kasar Sin wajen horo. Na kammala aiki a karon na farko game da kewaye duniyarmu cikin akwatin nazarin duniyar wata na kumbon Apollo a cikin yanayi mai kama da na zahiri, a karon na farko can a baya na samu fitowa daga akwatin gwaji. Kafin wannan aiki, mu ma mun samu horo a wata babbar na'urar da ake amfani da ita wajen horo tun tuni wato daga shekarar 1966 zuwa 1967, abin sha'awa ne a yau na samu damar kara ganin na'urar kusan iri daya a nan, dukkansu suna bin ka'idojin zahiri."

A yayin taron, hukumar kasar Sin ta yi bayani kan shirin ta a nan gaba, game da aikin da ya shafi kumbon da ke daukar 'yan sama jannati, inda ta ce za a kammala aikin kafa tashar sararin samaniya ta kasar Sin kafin shekarar 2022, wanda hakan ya jawo hankulan 'yan sama jannatin kasa da kasa. Koichi Wakata, 'dan sama jannati ne daga kasar Japan, ya bayyana cewa,

"Ina ta lura kwarai da ayyukan da kasar Sin ke yi a fannin sifirin kumbon mai dauke da 'yan sama jannati. A shekarar 2003, na hadu da dan saman jannatin kasar Sin Yang Liwei a birnin Tokyo, wanda ya shiga sararin samaniya, bayan haka kuma na ga fitowar 'dan jannati Zhai Zhigang daga kumbon Shen Zhou-7, ga shi kuma kasar Sin ta cimma nasarar harba kumbon Tian Gong-1. Gaskiya na yi farin ciki sosai kan nasarorin da Sin ta samu a fannin binciken sararin samaniya. Ina zura ido sosai ga ci gaba da Sin za ta samu a fannin a nan gaba. Ina kuma fatan shiga tashar sararin samaniyar kasar, saboda haka ne, ya zama wajibi na fara koyon Sinanci, amma lallai akwai wuyar koyo ga harshen."

Ba Koichi Wakata ne kawai ke koyon Sinanci bisa wannan buri ba, yanzu haka akwai 'yan sama jannati da yawa, dake koyon harshen sakamakon babbar shawarar da suke da ita kan shirin tashar sararin samaniya ta Sin. 'Yar sama jannati ta farko a nan kasar Sin, Liu Yang ta bayyana cewa,

"Yayin da nake cudanya da takwarorinmu, suna kyautata zato kan nasarar da tashar sararin samaniya ta Sin za ta samu bayan kammalar ta a nan gaba, sunafatan za su iya shiga ayyukanmu.Yanzu dai 'yan saman jannati na wasu kasashe, kamar su Italiya, da Burtaniya, da Amurka da dai sauransu na kokarin koyon Sinanci. Matakin da ke nuna cewa, yanzu kasar Sin tana da karfi ku san a dukkan fannoni."

A daya hannun kuma, batun yadda za a tsara wani nau'in bai daya game da kumbuna, shi ma wani muhimmin batu ne da aka tattauna a wannan taro.

Mataimakin daraktan ofishin kula da ayyukan tafiyar kumbon da ke dauke da 'yan sama jannati na kasar Sin, Yang Liwei ya bayyana cewa, a shekarar 2022 mai yiwuwa tashar sararin samaniya ta kasar Sin za ta kasance tasha daya tilo a sararin samaniya, a lokacin da za ta ba da karin amfanin da take da shi. Ta ce idan an tsara nau'in bai daya, to kumbuna na kasa da kasa za su iya sauka a tashar ta hanyoyi daban daban, kuma hakan zai taimaka wajen warware matsalolin da kumbunan kasa da kasa za su iya fuskanta, a lokacin da suke gudanar da bincike a sararin samaniya." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China