140917-Ranar-yaki-da-jahilci-ta-duniya-Sanusi.m4a
|
Manufar shirya wannan biki ita ce, ilimantar da jama'a da al'umma baki daya game da muhimmancin iya karatu da rubutu wato yaki da jahilci kamar yadda aka fi sani a galibin kasashen Afirka.
Alkaluma sun nuna cewa, akwai sama da mutane miliyan 700 da har yanzu ba su iya karatu da rubutu ba, sannan cikin mutane 5 akwai mutum a kalla guda da ake jin bai iya karatu da rubutu ba, sannan kashi 2 bisa uku na wannan adadi da muka ambata na wadanda ba su iya karatu da rubuntun ba mata ne.
Masana na danganta wannan matsala ta jahilci ko rashin iya karatu da rubutu da batun talauci, al'ada da rashin ingantattun manufofi ko tsare-tsare a bangaren hukumomin irin wadannan kasashe da abin ya shafa.
Manazarta na cewa, muddin aka gaza magance wannan matsala ta rashin iya karatu da rubutu a cikin al'umma, hakan na iya haifar da tarin matsalolin dake iya shafar bangarorin tattalin arziki, Ilimi, lafiya da sauran muhimman sassan ci gaban kasa. (Ibrahim/Sanusi Chen)