in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar Malamai ta kasar Sin
2014-09-11 17:24:09 cri

Ranar malamai ko "Teacher's Day" a Turance, rana ce da ake kebe wa don nazarin irin rawar da malamai suka taka ko suke taka wa, matsalolinsu, nasarorin da suka cimma ko nuna musu yabo ga irin gudummawar da suka bayar a bangaren ilimi wanda shi ne ginshikin zaman rayuwa na duniya..

Sai dai duk da muhimmancin wannan rana, kowace kasa tana da ranar da ta kebe don murnar wannan rana inda a wasu kasashe da yankuna a kan shirya shagulgulan a wannan rana mai muhimmanci ga bangaren ilimi. Yayin da a wasu kasashen ake shirya taruka da gabatar da jawabai, ko shirye-shirye na musamman a kafofin rediyo da talabijin a wasu kasashen kuma, dalibai ne kan baiwa malaman nasu kyaututtuka don nuna masu godiya da yabo saboda ilimin da suka ba su.

Sai dai duk da gudummawar da aka san malamai suna bayarwa ga ci gaban al'umma, har yanzu wannan sana'a ta malanta na fuskantar koma baya, ma'ana ba ta da daraja a wannan lokaci, sakamakon abin da masana ke dangantawa da nuna halin ko'in kula da mahukunta ke yiwa sana'ar.

Masharhanta na cewa, kamata ya yi hukumomi su samar da muhimman abubuwan da sana'ar malanta ke bukata, matakin da ake ganin zai taimaka baya ga bangaren na ilimi da a yanzu yake fuskantar matsala musamman a galibin kasashe masu tasowa.

A nan kasar Sin, an kebe ranar 10 ga watan Satumban kowace shekara, a matsayin ranar malamai, inda a bikin na bana, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bukaci malamai da su sadaukar da kai ga ayyukansu, ta yadda za a daga martabar ilimi a sassan kasar baki daya

Shugaba Xi ya kuma bukaci kusoshin JKS da sassan gwamnatoci a dukkan matakai, da su daukaka aikin koyarwa ko malanta ta yadda sana'ar za ta samu kimar da ta dace.

Masana na ganin cewa, akwai bukatar su ma malamai su martaba sana'ar ta malanta kana su tafiyar da aikinsu ta yadda zai dace da zamani. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China