140907-bikin-tsakiyar-kaka-2.mp4
|
A daren ranar 15 ga watan Agusta, a zamanin da, har zuwa yanzu, jama'ar kasar Sin kan yi addu'a ga wata yayin da suka daga kai sama suna kallonsa tare da cin wainar bikin tsakiyar kaka. Al'adar kallon wata ta fi samun karbuwa a zamanin daular Tang. A zamanin daular Song ta arewa, a daren ranar 15 ga watan Agusta, bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, dukkan gidaje, masu arziki, ko matalauta, kan yin addu'a ga wata tare da fada masa fatansu na alheri domin samun kariya daga gunkin wata. Ya zuwa zamanin daular Song ta kudu, jama'a kan mika wainar bikin ga juna domin saduwa da dangogi. Bayan zamanin daulolin Ming da Qing kuwa, al'adar ta samu karbuwa sosai a duk fadin kasar Sin.
An taba rubuta wata waka da ke bayani kamar haka: "Cikakken wata a sama, jama'a na murnar bikin tsakiyar kaka a ko ina." Yayin da ake murnar bikin, jama'a na begen iyalai a gari, kuma suna fatan za su sadu cikin sauri domin yin dariya da kuka tare da bayyanawa juna labaran zaman rayuwarsu. A cikin shekaru dubbai da suka gabata, bikin tsakiyar kaka ya samarwa jama'ar kasar Sin tsarin al'adu na musamman.
Saminu Alhassan dauke da wani karamin bidiyo, sai ku biyo mu cikin shirin. (Tasallah & Maryam)