in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ko kun san Bikin Tsakiyar Kaka na kasar Sin ? (1)
2014-09-07 17:03:58 cri

 

Jama'ar kasar Sin kan yi shagulgulan bikin tsakiyar kaka ne a ranar 15 ga watan Agusta, bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, ana kiran bikin da suna "bikin tsakiyar kaka" ne domin bikin ya kasance a tsakiyar yanayin kaka. An fara bikin ne a zamanin daular Tang, kuma shi ne babban biki na biyu a kasar Sin bayan bikin bazara, kawo yanzu, tarihin bikin ya kai shekaru sama da dubu daya.

Bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, shekara guda na kunshe da fasali hudu, kuma ko wanen fasali na kunshe da sassa uku. A daren ranar tsakiyar kaka, wata kan cika, sannan wata na haskaka ko ina, shi ya sa, a kan mayar da cikar wata a matsayin alama ta saduwar iyalai, har a kan mayar da ranar 15 ga watan Agusta a matsayin ranar saduwar dangogi, sakamakon haka, bikin tsakiyar kaka ya zama "bikin saduwa".

Saminu Alhassan dauke da wani karamin bidiyo, sai ku biyo mu cikin shirin. (Tasallah & Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China