140829-Yara-sun-yi-girma-yadda-ya-kamata-a-wani-kauye-mai-suna-SOS-da-ke-ba-da-taimako-ga-yara-Danladi
|
A shekarar 1996, an fara shirin kafa wani kauye mai suna SOS da ke ba da taimako ga yara a garin Putian na jihar Fujian da ke kudancin kasar Sin, a shekara ta 2000, an bude shi ne cikin nasara. A cikin kauye ne, an karbi wasu yara da suka raya iyalansu wadanda suka shiga cikin mawuhalin halin a zaman rayuwa, amma a wannan kauye ne, an ba su taimako, sun yi girma yadda ya kamata.
Shugabar kauyen Madam Zeng Suqiong ta gaya wa wakilinmu cewa,
"A kauyenmu, muna da malaman musamman, wadanda su kan yi cudanya da malaman da ke makarantun da wadannan yara ke karatu, mu kan gaya musu cewa, kada a ce wadanna yara ba su da iyalai, kada a bata zuciyarsu, idan suna son ba su taimako, sai su yi a boye, kada su yi farfaganda, domin kada wadanna yara sun bata zuciya."
Tsohon shugaban kungiyar kafa kauyukan ba da taimako ga yara na SOS na kasa da kasa Helmut library ya gaya wa manema labaru na kasar Sin cewa, kauyen SOS ba kawai ya ba da taimako ga yara a kan kudi ba, a'a, har ma ya kan mai da hankali kan kulawa da zuciyar yara, da kara karfin zuciyarsu yayin da suke shiga cikin al'ummomi. (Danladi)