140822-Yara-Kauyuka-da-birane-sun-yi-zama-tare-a-lokacin-huku-na-yanayin-zafi-Danladi
|
A watan Austa wato yaran suna lokacin hutu ba su je makaranta, babbar hukuma mai kula da madaba'a da watsa labarai ga yara ta kasar Sin ta shirya bikin hada kai a tsakanin yaran kauyuka da birane, wanda aka shafe kwanaki 5 ana yinsa.
Wannan aiki ya mai da hankali kan inganta mu'ammala da ke tsakanin yaran da ke zama a kauyuka da birane, hukumar ta kira yara 30 daga kauyukan jihohin Shandong, da Sichuan, da Guizhou, da Hubei, da Zhejiang da dai sauransu, domin su zama tare da yara 30 da suka zo daga birane, sabo da haka ne wadannan yara suna iya zama tare da karatu tare.
Game da wasu yara, karo na farko ne da suka zo birnin Beijing, sabo da haka ne suna jin murna sosai, yaran Beijing sun zama masu jagoranci, sun yi yawon shakatawa tare da abokansu a titunan Hutong, da jiragen da ke karkashin kasa, da cin abincin musamman na Beijing, da kuma fahimtar tarihi da al'adun gargajiya na kasar Sin. (Danladi)