in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin BAD ya shawarta shirin yaki da zamba da cin hanci
2014-08-20 10:53:14 cri

Bankin cigaban Afrika (BAD) ya bukaci kasashen dake amfani da harshen Portugal (PALOP) a matsayin harshen aiki da su dauki matakin kin nuna sassauci ga masu aikata zamba da cin hanci ta hanyar dokokin shari'a da na hukumomi domin samar da tsarin mulki na gari da kuma adalci cikin hukumomin gwamnati.

Mista Ezzeddine Nciri, jami'in dake kula sashen dunkulewa da yaki da cin hanci na bankin BAD ya shawarta wannan ra'ayi a kwanan nan a birnin Praia a yayin wani taron karawa juna sani zuwa ga 'yan majalisu da kwararrun kasar Angola, Cap-Vert, Guinee-Bissau, Mozambique da Sao Tome and Principe.

Taron karawa juna sanin ya mai da hankali kan matsayin 'yan majalisu a bangaren bunkasa tsarin mulki na gari, tafiyar da harkokin kudi a cikin ma'aikatun gwamnati da kuma tislasta gabatar da rahoton aiki.

A cewar mista Nciri, bankin BAD ya cimma wata manufar kin nuna sassauci da duk wasu ayyukan cin hanci da na sumogal. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China