in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yadda cutar Ebola ke barazana ga duniya
2014-08-29 17:03:36 cri

Ebola wata kwayar cutar virus ce wadda alamun kamuwa da ita na farko suka hada da zazzabi mai zafin gaske da kasala mai karfi da ciwon gabobi da rikewar makogwaro. Sai matakin cutar na gaba wato amai da gudawa da kuma a wasu lokuta, zubar jini a ciki da kuma jiki.

Masana harkar lafiya sun bayyana cewa, kwayoyin cutar kan dauki tsawon kwana biyu zuwa makonni uku kafin su kyankyashe, kuma kula da wadanda suka kamu da cutar yana da matukar hadari domin a mutum na iya kamuwa da cutar.

Cutar Ebola na yaduwa a tsakanin mutane ne ta hanyar ta'ammali da dabbobin da suka kamu da cutar irinsu gwaggon Biri da Jemage har ma da Gada.

An fara gano cutar Ebola ce a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo a shekarar 1976 tun lokacin ne kuma cutar ta ci gaba da yaduwa a tsakanin kasashen gabashin Afirka ciki har da Uganda da Sudan, sannan ta bulla a kasar Guinea a watan Fabrairu inda take ci gaba da yaduwa a sassan kasar.

Yanzu haka cutar Ebola ta halaka mutane sama da 1,000 tun bayan da cutar ta bulla a kasashen yammacin Afirka da suka hada da Liberia, Guinea, Saliyo da kuma wasu kalilan a Najeriya. Wannan ya sa wasu kasashen da ke makwabtaka da wadannan kasashe da ke fama da wannan cuta daukar wasu matakai da suka hada da rufe kan iyakokinsu, dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa kasashen ko daukar fasinjojin da suka fito daga wadannan kasashe.

Hukumar lafiya ta duniya WHO da wasu kasashe, ciki har da kasar Sin sun aike da taimakon kayayyakin kiwon lafiya da tawagar ma'aikatan lafiya zuwa kasashen da suke fama da wannan cuta.

Kwamitin kwararru na hukumar lafiya ta duniya WHO sun yanke shawarar amfani da magungunan gwaji ga wadanda suka kamu da cutar ta Ebola.

Yanzu dai cutar Ebola mai saurin kisa ba ta da magani, don haka ma'aikatan lafiya ke kira ga jama'a da su kara daukar matakan kariya daga kamuwa da cutar, yayin da gwamnatocin kasashen da ke fama da cutar ke kara fadakar da jama'a tare da ware makuden kudade don tunkarar wannan cuta da yanzu haka ta kasance mafi hadari a duniya. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China