140820-Yadda-masana-ke-kallon-taron-kolin-Amurka-da-Afirka-Sanusi
|
Shi dai wannan taron koli, ya zo ne a dai-dai lokaci da shugaba Obama na Amurka ya mayar da hankali kan nahiyar Afirka a wa'adi na biyu na mulkinsa don cin gajiyar albarkatun tattalin arzikin da Allah ya hore wa nahiyar, inda ya bayyana shirinsa na bunkasa harkokin cinikayya tsakanin kasar ta Amurka da nahiyar Afirka yayin rangadin da ya kai kasashen Afirka uku a shekarar 2013.
An kuma shirya ganawar ce bisa taken "zuba jari a cikin zamanin da ke tafe" tare da mayar da hankali kan harkokin cinikayya da zuba jari, inda ake saran kamfanonin Amurka za su zuba jarin dala biliyan 14 a bangaren makamashi da samar da ababen more rayuwa, sannan ana sa ran sanar da kulla wasu yarjejeniyoyi a bangaren aikin gona, abinci da kuma makamashi.
Sai dai wani abin takaici shi ne, duk da muhimmancin wannan taro ba a shirya wata ganawa tsakanin shugaba Obama da shugabannin na Afirka ba. Sanin kowa ne cewa, a kullum kasar Sin ta kan dauki manufar sada zumunci da nuna sahihanci, daidaici da adalci, kawo moriyar juna da samun bunkasuwa gaba daya kan nahiyar Afrika. Wannan ya sa masana ke fatan Amurka za ta daidaita matsayin da take dauka kan bunkasuwar kasar Sin da aikin da take yi na zuba jari a Afrika.
Bugu da kari masu sharhi na cewa, duk wadannan matakai da Amurka ke dauka na zuwa ne a yayin da Sin ke kara zuba jari a nahiyar, matakin da masu fashin baki ke cewa, lokaci ya yi da al'ummar nahiyar ta Afirka za su bambance tsakanin tsaki da tsakuwa. (Ibrahim/Sanusi Chen)