in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya wani bikin aure bisa tsarin Musulunci a gundumar Ludian
2014-08-13 15:56:21 cri

A ranar 11 ga wata da dare, aka shirya wani bikin aure bisa tsarin Musulunci a gidan iyalan ango. Ba a kawata zauren gidan sosai ba, sai dai an manna wata takarda mai dauke da kalmar "Alheri" a bangon dakin. Iyalai fiye da 30, ciki har da dattijo mai shekaru 80 da haihuwa, da jaririn da ya kai shekara 1 da wani abu, sun cika dakin da bai kai murabba'in mita 10 ba. Amarya Ma Xiuping wadda ta yi ado da nikaf mai launin ja da angonta wanda ya sa farar hula sun zauna tare. Limanin masallacin Wenping na gundumar Ludian, Ma Zhongwei ya karanta musu wasu ayoyin "Alkur'ani". Wannan shi ne karo na farko da limami Ma Zhongwei ya shugabanci wani bikin aure tun bayan da bala'in girgizar kasa ya auku a gundumar Ludian. Ya gaya wa manemin labaru kamfanin dillancin labaru na Chinanews, cewar a daidai lokacin aukuwar bala'in girgizar kasa, yana shugabantar wannan bikin aure.

 

 


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China