140811-musayar-aladu-dake-tsakanin-sin-da-afrika-bako
|
Kwanan baya, an bude wani taro na horar da jami'an kasashen Afrika game da zane-zanen cartoon, da shirye-shiryen telebijin a birnin Tianjin da ke kasar Sin. Jami'an kasashen Afrika ta Kudu da Nijeriya guda 9 sun halarci taron. Francis ya kasance daya daga cikinsu, yayin da yake zantawa da wakilinmu Bako, ya bayyana cewa, musayar al'adu dake tsakanin kasashen Sin da Afrika zai habaka hadin gwiwa daga dukkan fannoni a tsakaninsu.(Bako)