140808-ranar-masoya-ta-Sinawa-lubabatu
|
Kamar yadda kowa ya sani, ranar 14 ga watan Faburairu ranar masoya ce bisa al'adun al'ummar kasashen yammaci. Ban da Turawa, sauran al'ummomin duniya su ma suna da al'adu na kusa da suka shafi ranar masoya, sai dai ya yiwu a rana ta daban, kuma ta hanyoyi na daban ne ake wannan rana. A nan kasar Sin, al'ummar kasar sun kebe ranar 7 ga wata na bakwai na kowace shekara, bisa kalandar gargajiyarsu, a matsayin ranar masoya, ko kuma mu ce "Qixi" da harshen Sinanci. Domin samun karin haske, sai a biyo mu cikin shirin.(Lubabatu)