in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi game da jirgin Malaysia da ya fadi a Ukraine
2014-08-10 16:19:59 cri

A ranar Jumma'a 18 ga watan Yuli ne jirgin saman fasinja na kasar Malaysia mai lamba MH17 da ke dauke da fasinjoji 280 da kuma ma'aikatan jirgin 15 ya tarwatse a yankin Ukraine kusa da kan iyakar kasar Rasha.

Jirgin na Malaysia kirar Boeing 777 wanda ya taso daga birnin Amsterdam na kasar Holland a kan hanyarsa ta zuwa Kuala Lumpur na kasar Malasiya ya bace a na'urar rada a nisan mita 10,000 a sararin samaniya, sannan ya fado a kusa da Chakhtarsk da ke yankin Donetsk na kasar Ukraine.

Wannan shi ne jirgin saman kasar Malaysia na biyu da ya yi hadari a wannan shekarar ta 2014, bayan wanda ya yi batan bado a ranar 8 ga watan Maris a kan hanyarsa ta zuwa birnin Beijing daga Kuala Lumpur dauke da fasinjoji kusan dari 3, galibinsu Sinawa.

Rasha da Ukraine na zargin juna game da faduwar jirgin na Malaysia samfurun MH17, yayin da a hannu guda kuma Rasha ke fuskantar matsin lamba daga sassan duniya tun lokacin faruwar wannan hadari.

Sai dai ma'aikatar harkokin tsaron Rasha ta ce na'urorinta sun ga makaman kakkabo jiragen sama na kasar Ukraine suna shawagi a yankin sararin samaniyan da aka harbo jirgin.

Shugaba Putin na Rasha ya bayyana aniyar kasarsa na samar da tallafin da ya wajaba na gano musabbabin faduwar jirgin. Yanzu haka an kafa wata tawaga da ta kunshi jami'an Holland da Malaysia da wakilan cibiyar binciken hadarrukan jiragen sama ta kasar Burtaniya, gami da hukumar tsaron harkokin sufuri ta kasar Amurka don binciken dalilin hadarin.

A nasa bangaren, kwamitin sulhu na MDD ya zartar da wani kuduri da ke matukar nuna takaici game da faduwar jirgin, sannan ya kalubalanci sassan da abin ya shafa da su taimaka ga aikin binciken musabbabin faduwar jirgin wanda tawagar kasa da kasa ke jagoranta.

Kudurin ya kuma bukaci a mutunta gawawwakin wadanda suka rasu, ta yadda za a mika su ga iyalansu cikin mutunci.

Masu sharhi na ganin cewa, akwai sakacin hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta duniya na rashin rufe hanyar sararin saman na Ukraine ga jirage saboda hadarin da ke tattare da bin hanyar, sakamakon fadan da ake yi a yankin da kuma yadda a baya aka harbo wasu jiragen da har yanzu bangarorin biyu ke zargin juna da aikatawa.

Yanzu ana ganin cewa, shiga tsakanin da MDD ta yi na iya kawo karshen duk wani cikas da ake fuskanta game da gudanar da cikakken bincike a wurin da hadarin ya faru.

Abin jira a gani shi ne, sakamakon binciken da kuma hukuncin da za a yanke wa bangaren da aka samu da hannu a harbo jirgin na Malaysia. (Ibrahim/Sanusi chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China