140806-Bikin-karamar-sallah-a-nan-kasar-Sin-Sanusi
|
Kamar sauran kasashen musulmi na duniya haka ma a nan kasar Sin, musulmi suka yi tururuwa zuwa masallatai da ke wurare daban-daban a wannan rana don gudanar da sallah mai raka'a biyu suna sanye da sabbin tufafi cikin farin ciki da annashuwa.
Sai dai ba kamar yadda aka saba hawan daba ko dawakai a lokutan sallah a kasashenmu na Afirka inda ake kade-kade da bushe-bushe a irin wannan rana, a nan lamarin ya sha bambam kamar yadda masu iya magana ke cewa, "Allah daya gari bambam". Sai dai su ma musulmi da ke nan kasar Sin kan yi irin nasu shagulgulan da gaishe-gaishe da nau'o'in abinci da ake dafawa don murnar wannan rana.
Abu mai muhimmanci a nan Sin shi ne yadda ake samar da matakan tsaro a ranakun sallar Azumi da Lahiya da ma sauran lokutan da musulmi ke gudanar da salloli a masallatai a duk fadin kasar ta Sin.
Amma duk da irin bambancin da ke akwai, musulmi 'yan kasashen waje da ke nan Sin sun yi karamar sallah cikin farin ciki sai dai abin da ba za a rasa ba na kadaici, kuma masu salon magana na cewa, sallah bikin daya rana, ta tafi ta bar wawa da bashi
Sai kuma wata shekara ga mai sauran numfashi, Allah ya maimaita mana da alheri, Amin. (Ibrahim/Sanusi Chen)