A ranar Laraban nan, kasar Sin ta sake shawarci al'ummarta dake kasar Libya da su dawo gida ba tare da bata lokaci ba, ganin yadda yanayin tsaro ya tabarbare a kasar.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar a cikin wata sanarwa ta ce, tashin hankali da ake yi da makamai a Libya ya tabarbare, sannan kuma yanayin tsaro yana da hadari matuka, don haka ake shawartar al'ummar Sinawa a Libyan da su dawo gida tare da alkawarin ba su dukkan taimakon da ya kamata na ganin hakan ya faru.
Ma'aikatan ofishin jakadancin kasar dake Libyan su ma za'a dawo da su gida sannu a hankali, in ji sanarwar da aka buga a shafin yanar gizon ma'aikatar. (Fatimah)