140723-Kasashen-BRICS-na-shirin-kafa-bankin-raya-kasa-Sanusi
|
Wata sanarwar da aka fitar yayin taron shugabannin da ya gudana a kasar Brazil ta nuna cewa, hedkwatar sabon bankin za ta kasance ne a birnin Shanghai na kasar Sin, yayin da ake sa ran zuba masa jarin da ya kai dalar Amurka miliyan dubu 100 sannan za a bude ofishin shiyyar bankin ta Afirka a kasar Afirka ta Kudu, yayin da shugaban bankin zai kasance dan kasar Indiya.
Manufar kungiyar ta BRICS ta kafa bankin raya kasa, wanda zai fara aiki da jarin dalar Amurka miliyan dubu 100, ita ce baiwa kasashe mabukata, musamman masu tasowa damar kaucewa fadawa matsalolin kudi da samar da rance domin rage kaifin matsalolin tattalin arziki. Har wa yau ana fatan wannan tsari zai taimaka wajen kara hada kan kasashe mambobin kungiyar tare da baiwa tsarin tattalin azikin duniya kariya ta musamman bisa tsare-tsaren da ake da su a halin yanzu.
A shekarar 2001 ne, Jim O'Neill, babban masani kan tattalin arziki dake aiki a kamfanin Goldmansachs na Amurka ya fara tunanin wannan ra'ayi na "Kasashen BRICS" a karo na farko a duniya. A watan Yuni na shekarar 2009, shugabannin kasashen BRICS suka yi ganawar farko a hukunce a kasar Rasha. Daga bisani, a watan Disamba na shekarar 2010, kasashen na BRICS suka cimma matsaya daya wajen shigar da kasar Afirka ta Kudu cikin kungiyar.
Masana na ganin cewa, wannan manufa ta BRICS, za ta taimaka wajen daga matsayin kasashen kungiyar na yada manufofi da tunaninsu a harkokin duniya, baiwa kasashe masu tasowa ikon fadin albarkacin baki da kuma shimfida yanayi mai kyau ga tattalin arzikin duniya. (Ibrahim, Sanusi Chen)