in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Afirka na kokarin karfafa hadin kai ta fuskar kiyaye muhalli
2014-07-21 22:13:53 cri

Ana ta samun saurin bunkasuwar tattalin arziki a duniya, hakan ya sanya kasar Sin ko kasashen Afrika dukkansu suke fuskantar matsalolin gurbacewar muhalli da rashin albarkatun kasa sakamakon ci daban masana'antu, birane a fadin duniya. Bisa wannan yanayin da ake ciki, akwai bukatar a hanzarta neman wata hanyar bunkasuwa mai dorewa. Yanzu dai kasar Sin da kasashen Afrika suna kokarin daga matsayinsu na kiyaye muhalli da kara hada kai a bangaren fasahohi a wannan fanni.

Kasar Sin da kasashen Afrika suna da dogon tarihi wajen hada kai ta fuskar kiyaye muhalli. Tun lokacin da aka gudanar da taron kula da muhallin dan Adam na MDD da aka shirya a shekarar 1972, bangarorin biyu suka soma hadin kai mai amfani cikin dogon lokaci, wanda ya kiyaye moriyar kasashe masu tasowa. Bayan da aka shiga sabon karni, bisa dandalin tattaunawar hadin kai a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ne, bangarorin biyu suka tabbatar da wasu fannoni masu muhimmanci da manufofinsu game da kiyaye muhalli. A watan Yuni na shekarar 2014, an daga matsayin majalisar hukumar kula da muhalli ta MDD zuwa babban taron muhalli na MDD wato UNEA, tun daga lokacin ne Sin da kasashen Afrika suka karfafa hadin kai a tsakaninsu a fannin kiyaye muhalli.

A yayin babban taron UNEA karo na farko, an shirya taron tattaunawa na ministoci game da hadin kan kiyaye muhalli tsakanin Sin da kasashen Afrika, inda mataimakin magatakardan MDD, kuma daraktan zartaswa na hukumar tsare-tsaren kiyaye muhalli Achim Steiner ya yi jinjina sosai kan kokarin da Sin ke yi wajen kiyaye muhalli, ya kuma jaddada cewa, matakan da kasar Sin ke dauka wajen tinkarar matsalolin kiyaye muhallinta ya kasance misali ga dukkan sassan duniya. Kazalika kuma ya nuna babban yabo ga tsarin tattaunawar ministoci, ya ce,

"Taron ministoci game da hadin kan kiyaye muhalli tsakanin Sin da kasashen Afrika yana da ma'ana sosai, karfafa hadin kai da mu'amala tsakanin sassan biyu zai tamaka wajen inganta bunkasuwar tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba a kasashe masu tasowa. Hukumar tsare-tsaren kiyaye muhalli ta MDD ta shafe sama da shekaru 40 tana hada kai tare da Sin a wannan fanni, muna sa ran ganin karfafa irin wannan hadin kai tare da Sin a duk fadin duniya."

Batun karfafa matsayin hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afrika wajen kiyaye muhalli, wanda aka gabatar a yayin taron tattaunawar, ya nuna sabbin alamu ta fuskokin manufofin hadin kai, da bullo da wasu dandamala, inda aka jaddada kafa manyan dandamala guda uku, wato yadda za su rika tattauna manufofi, da karfafa kwarewa da kuma yin cudanyar fasahohi. Yayin da yake gabatar da shawara kan hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afrika kan kiyaye muhalli a nan gaba, ministan kiyaye muhalli na kasar Sin, Zhou Shengxian ya nuna cewa,

"Ya kamata bangarorin biyu su kara tattauna wa da hada kai a fannonin kyautata muhallin birane, kiyaye muhallin halittu, gudanar da cinikayya ba tare da gurbata muhalli ba, da zuba jari da dai sauransu, don ciyar da hadin kansu wajen kiyaye muhalli gaba. Mun ba da shawarar aiwatar da shirin kiyaye muhalli tsakanin Sin da kasashen Afrika, wanda ya kasance daya daga cikin sassan ayyukan hadin kai da Sin za ta gudanar game da kiyaye muhalli tsakanin kasashe masu tasowa, ta yadda za mu ji gajiyar fasahohin da aka samu a fannin kiyaye muhalli, da karfafa kwarewa a fannin, da kuma karfafa wa jama'a kwarin gwiwar kiyaye muhalli. Kasar Sin ma na fatan samar da iyakacin taimako don karfafa karfin kasashen Afrika na kiyaye muhalli, da kuma ba su horo."

Wasu kungiyoyi da jami'ai dake kula da harkokin kiyaye muhalli na Afirka sun nuna yabo ga nasarorin da Sin ta samu wajen bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, da kuma tinkarar kalubale dake da nasaba da aikin kare muhalli, da dai sauransu. A ganinsu, tsarin da kasar Sin ke bi na neman sabuwar hanyar kiyaye muhalli, ya dace kasashen Afrika su yi koyi da shi. Mataimakin shugaban taron ministocin kula da harkokin kiyaye muhalli na kasashen Afirka, kuma ministan kula da harkokin kiyaye muhalli na kasar Masar, Khaled Fahm Abdel Aal ya bayyana cewa, ya kamata kasar Sin ta yiwa kasashen Afrika jagora a fannin kiyaye muhalli:

"Mu koyi fasahohin bunkasuwa daga wajen kasar Sin, kamar yadda wani karin magana na Sinawa ke cewa, 'koya wa mutum kamun kifi ya fi ka baiwa mutum kifi kai tsaye'. Muna fatan Sin za ta kara koya mana fasahohi. Muna da imanin cewa, tattaunawar za ta kara fahimtar juna tsakanin Sin da kasashen Afirka, da kuma zurfafa hadin kai tsakanin bangarori da dama, da inganta gudanar da wasu ayyukan da abin ya shafa." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China