140725-Azumin-Ramadan-na-Musulman-jihar-Xinjiang-ta-kasar-Sin-Danladi
|
A 'yan kwanakin baya, gidan rediyon kasar Sin ya shirya wata tawaga da ke kunshe da wakilai na Sin da waje don kai ziyara a jihar Xinjiang ta kasar Sin, a daidai ziyararsu, sun gamu da bikin gargajiya na Musulmai wato azumin Ramadan, wannan dai ya ba wakilanmu damar fahimtar hanyoyin da Musulman Xinjiang suke bi yayin bikin.
Da wakilinmu ya yi mu'ammala sosai da wasu shugabannin addinin Musulunci a Xinjiang. Yayin da wakilinmu yake amtaba cewa, "yaya Musulman Xinjiang suke bikin Azumi?" Wani musulmi mai suna Yakupcan ya ce, daga ranar 29 ga watan Yunu ne, Musulmai na Xinjiang sun fara azumi, za su yi a gida ko a masallaci.
Tambaya ta biyu ita ce, ta wace hanya, Musulmai matasa na kabilun Uygur da Kazakh da Uzbek da dai sauran kananan kabilu da ke zama a Xinjiang suke bi wajen karbar ilmin addini? Game da haka, Yakupcan ya ce, yana da muhimmanci da a karbi horo a gida kafin da a karbi ilmin addini na hukunce, matasa wadanda shekarunsu sun wuce 18 da haihuwa za su iya je masallaci bisa burinsu domin karbar ilmin addinai a hukunce.
An yi tambaya ta uku cewa, ko a kayyade ma'aikatan gwamnati da dalibai wajen yin azumi? Wani liman mai suna Aysancan ya ce, a'a. Ya ci gaba da cewa, kasar Sin tana aitawar da manufofin cikin 'yanci ga addinai, ko dalibai ko ma'aikatan gwamnati suna iya yin azumi bisa ga burinsu, ba a kayyade su ko kadan ba. Wasu kafofin watsa labaru sun bayar da wasu labarai ba tare da shaidu kuma kurkure ne.
Shugabannin addinin Musulmai sun gaya mana cewa, musulman Xinjing ciki har da 'yan kabilar Uygur da Kazakh da Uzbek da dai sauran kananan kabilu suna zama cikin jituwa a Xinjiang, babu bambanci a tsakaninsu. (Danladi)