140718-Zaman-jituwa-a-tsakanin-kabilu-daban-daban-a-Xinjiang-Danladi
|
A 'yan kwanakin baya, gidan rediyon kasar Sin ya shirya wata tawaga da ke kunshe da wakilai na Sin da waje don kai ziyara a jihar Xinjiang ta kasar Sin, a ziyararsu, sun ga jama'ar kabilu daban daban suna zama cikin jituwa a garin Ghulja na jihar Xinjiang ta kasar Sin.
Garin Ghulja ya taba zama wani babban gari a fannonin tattalin arziki da kasuwanci a arewa maso yammacin kasar Sin, wanda duwatsu ke kewayensa. A wannan gari, ana iya ganin abubuwan kasa da kasa. Ana iya ganin suga na kasar Rasha, ana iya ganin chokali na kasar Kazakhstan, haka kuma ana iya ganin tafuffin irin na India da Gabas ta Tsakiya, a nan wuri kuma muna iya saurarar harsuna daban daban.
Hadin kai a tsakanin kabilu daban daban ya burge wakilinmu kwarai da gaske. A ziyararsu, sun ga 'yan kabilu da yawa a Xinjiang. Wani abin da ya fi ba da muhimmanci shi ne, ko da yake wadannan 'yan kabilu suna da harsuna na daban, suna da tufafi na daban, suna da al'adu na daban, amma suna iya zaman jituwa da juna. Sabo da haka ne, wakilanmu sun yi imani cewa, zaman jituwar 'yan kalibu a Xinjiang ya shaida cewa, kasar Sin wata kasar ce mai girma da ke da al'adu iri daban daban, Sinawa sun nuna girmamawa ga kabilu daban da al'adu daban. (Danladi)