in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala gasar cin kofin duniya da aka yi a Brazil
2014-07-17 19:30:37 cri

A ranar Lahadi 13 ga watan Yuli ne aka kammala gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya na shekarar 2014 a kasar Brazil, gasar da aka kwashe wata guda cur ana yi, inda kasar Jamus ta lashe kofin bayan da ta doke Argentina da ci 1 da nema a wasan karshe.

Wannan shi ne karo na 4 da kasar ta Jamus ta lashe kofin a tarihin gasar, inda ta lashe kofin a shekarar 1954, 1974, 1990 da shekarar 2014.

Bayanai daga shafin hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA na nuna cewa, an sayar da tikitin shiga gasar da aka gudanar a filayen wasa daban-daban guda 12 a kasar Brazil kimanin miliyan 3 a gasar ta wannan shekara, inda 'yan kasar Brazil suka sayi kashi 60 cikin 100 na tikitin, yayin da 'yan kallo daga sassa daban-daban na duniya suka sayi kashi 40 cikin 100.

Koda yake kasar Amurka ce ke kan gaba wajen sayen tikitin, sai kasar Argentina, Jamus, Ingila, Columbia, Australia, Chile, Faransa, Mexico da dai sauransu. Masu fashin baki na cewa, hakan na da nasaba da sha'awar wasanni da kuma karfin tattalin arzikin wadannan kasashe.

Bisa tsarin hukumar FIFA, duk kasar da ta halarci gasar za ta tashi da kyautar tsabar kudi dala miliyan 1.5, yayin da kasar da ta lashe kofin za ta samu kyautar kudi wuri na gugan wuri har dala miliyan 35, kasar da ta zo ta biyu za ta samu dala miliyan 25, kasa ta uku dala 20 yayin da kasar da ta zo ta hudu za ta samu kyautar dala 18.

A karshen gasar kamar sauran gasannin da suka gabata, an bayar da lambobin yabo, wadanda suka hada da kwallon zinare wanda ake baiwa dan wasan da ya fi kwazo da takalmin zinare da ake baiwa dan wasan da ya fi zura kwallaye a gasar, sai safar zinare da ake baiwa mai tsaron gidan da ya fi kwazo.

A wannan karo Lionel Messi dan kasar Argentina ne ya lashe kyautar kwallon zinare, sai James Rodriguez dan kasar Colombia wanda ya lashe kyautar takalmin zinare, yayin da mai tsaron gidan Jamus Manuel Neuer ya samu safar Zinare kana Paul Pogba dan wasan kasar Faransa ya samu kyautar matashin dan wasa mafi kwazo a gasar, kana kasar Colombia ta kasance kasar da ta fi wasa mai tsafta a gasar ta bana.

Kamar yadda hukumar FIFA ta tsara kasar Rasha ce za ta dauki bakuncin gasa ta gaba da za a gudanar a shekarar 2018 ga mai sauran numfashi. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China