140709-Rawar-da-kasashen-Afirka-suka-taka-a-gasar-cin-kofin-FIFA-a-Brazil-Sanusi
|
An bayyana gasar ta bana da ke gudana a Brazil da cewa ita ce gasa mafi kayatarwa a tarihi, inda aka karya tarihi ko bajintar da aka kafa a baya, kamar a bangaren kwallayen da aka zura, shafukan sada zumunta irin su facebook, Twitter da sauransu inda biliyoyin masu sha'awar kwallon kafa suka rika tabka muhawara a lokacin da ake wasa.
Sai dai duk da irin wadannan ci gaban da aka samu a wannan gasa ta Brazil, abin takaici shi ne kasashen Afirka da suka wakilci nahiyar a wannan gasa, irin su Najeriya, Ghana, Kamaru, Aljeria, da Cote d'Ivoire ba su tabuka rawar a zo a gani ba, har ma a kai ta samun wasu matsaloli da suka kunno kai a gida tun ma kafin a fara gasar ta Brazil.
Matsalar da ta bayyana a fili ita ce ta batun kudaden alawus din 'yan wasa, inda a wasu lokutan 'yan wasan kasashen Afirka suka yi baranazar kin halartar gasar, wasu ma kan ki halartar atisayen horaswa a lokacin da suke Brazil din. Wadannan matsaloli da wasu sun taimaka wajen hana kasashen na Afirka taka rawar da ta dace a irin wadannan gasanni.
Sai dai duk da cewa, kasashen na Afirka ba su wata taka rawa a gasar ba, amma akwai 'yan wasan Afirka wato dan kasar Ghana Asamoah Gyan da ya kasance dan Afirka da ya fi kowa zura kwallo a tarihin gasar
Masu sharhi na ganin cewa, muddin ana bukatar hana aukuwar hakan nan gaba, wajibi ne a samu tsari mai inganci da zai magance wannan matsala ta batun alawus din 'yan wasa, zabar 'yan wasan da suka kamata da sauran batutuwa da ke shafar rawar da kasashen Afirka ke takawa a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya.
Bugu da kari, irin sabbin matakai da fasahohin zamani da hukumar FIFA ke bullo da su a tsarin gasar, na sanya wasan kwallon kafa da ke kara hada kan al'ummar duniya kara samun karbuwa a wajen jama'a. (Ibrahim/Sanusi Chen)