in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimmancin manufar zama tare cikin lumana ga ci gaban duniya da kasashen Sin,Indiya da Myammar suka gabatar
2014-07-14 18:14:55 cri

A ranar 28 ga watan Yuni ne a birnin Beijing na kasar Sin kasashen Sin, Indiya da Myammar suka yi bikin cika shekaru 60 da sanar da manufar nan ta zama tare cikin lumana da shugabannin wadannan kasashe suka kaddamar a shekarar 1954.

Wannan manufa za ta bayyana wani matsayi mai karfi yayin da duniya ke fuskantar sauye-sauye, wadda kuma za ta ba da sabuwar gudummawa wajen kafa wata sabuwar dangantakar kasa da kasa da ke nuna daidaici da adalci da amincewa da juna, da yin hakuri da juna tare da kawo moriyar juna.

Wadannan manufofi guda biyar wadanda suka hada da mutunta 'yancin kasa da yankunanta, rashin tsoma baki a harkokin cikin gidan juna, mutunta juna da cin moriya tare da zama cikin lumana, an gabatar da su ne cikin wata sanarwar da aka bayar a taron kasashen Asiya da Afirka da aka gudanar a Bandung na kasar Indonesia a watan Afrilun shekarar 1955.

Masu sharhi na ganin cewa, wadannan manufofi za su taimaka wajen warware wasu batutuwa tsakanin Sin da wasu kasashe da ke kudu maso gabashin Asiya a teken kudancin Sin da kuma wasu muhimman batutuwa na kasa da kasa.

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin a jawabin da ya yi yayin bikin tunawa da wannan rana wanda ya janyo hankalin kasa da kasa ya jaddada cewa, kamata ya yi a mutunta 'yancin kasa da cikakkun yankunanta da zabin tsarin zaman rayuwa da salon bunkasuwarta, sa kaimi ga samar da zaman lafiya a duniya, rashin tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashe da dai sauransu.

Masu fashin baki na ganin cewa, tsoma bakin kasashen yamma kan harkokin cikin gidan wasu kasashe da irin wadannan manufofi masu tasiri, su ne ke kawo cikas ga duk wani kokari na samar da zaman lafiya har ma da ci gaba a duniya.

Don haka, muddin ana bukatar a zauna tare cikin lumana a duniya, wajibi ne a bar kowace kasa ta tafiyar da harkokinta da kanta daga dukkan fannoni ba tare da tsoma bakin wata kasa ba, matakin da zai tabbatar da 'yancin kasa da cikakkun yankunanta, wanda daga karshe zai samar da zaman lafiya da wadata a duniya, domin masu iya magana na cewa, "zama lafiya ya fi zama dan sarki". (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China