in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rawar da kamfanonin Sin ke takawa ga ci gaban aikin gona a Afirka
2014-07-03 19:17:08 cri

Na duke toshon ciniki "Noma" sana'a ce da ke da dogon tarihi a rayuwar bil-adama wadda ke taimaka wa wajen samar da abinci da kudin shiga ga jama'a har ma da kasar da ta rungumi wannan sana'a ka'in da na'in.

Sai dai yayin da wasu kasashe da daidaikun jama'a suka baiwa wannan sana'a muhimmanci a wasu wuraren ba haka lamarin yake ba, duk da cewa, Allah ya hore wa wasu kasashen filayen noma masu dausayi, isasshen ruwan sama, hasken rana da kuma kwadagon da za su yi amfani da su wajen noma nau'o'in abinci.

Nahiyar Afirka tana daga cikin kasashen da Allah ya baiwa filayen noma, kwadago da isasshen ruwan sama, amma saboda ba su da fasahohi da kayayyakin noma na zamani, ko irin shuka masu inganci, wannan ya sa ba sa iya samun amfanin gona mai yawa.

Ko da ya ke hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka ta taimaka sosai wajen share wa manoman wasu kasashen Afirka hawaye. Misali akwai kamfanin Sin mai zaman kansa na Hefeng na lardin Hubei, ya zuba jari a fannin bunkasa aikin gona a lardin Sofala dake tsakiyar Mozambique da kuma kamfanin Wanbao wanda shi kuma ya mayar da hankali kan noman shimkafa, ba da jagoranci a fannin fasaha, sayen shinkafan da manoman yankin suka noma.

Wadannan shirye-shirye da kamfanonin Sin ke gudanarwa a kasashen Afirka sun taimaka wajen bunkasa aikin gona, samar da kudaden shiga ga manoma da kuma ayyukan yi ga al'ummomin wadannan wurare.

Masu fashin baki na ganin cewa, kamfanonin kasar Sin da ke gudanar da shirin bunkasa aikin gona a kasashen Afirka suna tabbatar da manufar hadin gwiwar Sin da Afirka na cin moriyar juna bisa tushen girmama juna, domin a gudu tare a tsira tare.

Don haka, kamata ya yi al'ummomin da ke cin gajiyar ayyukan wadannan kamfanoni su rungume su da hannu biyu-biyu, sannan su ma gwamnatocin kasashen na Afirka su baiwa kamfanonin goyon baya ta yadda za a kara inganta irin wadannan shirye-shirye da nufin bunkasa aikin gona a nahiyar Afirka, domin noma shi ne tushen arziki. (Ibrahim, Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China