in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar Maman Ada zuwa garin Handan(2) Me ka  sani game da Handan?
2014-07-05 16:13:09 cri

Handan birnin ne da ke kudancin lardin Heibei a arewacin kasar Sin, wanda ke da fadin kilomita dubu 12 da kuma al'umma miliyan 9.63. Handan birni ne da ya shahara da dadadden tarihinsa, inda tun shekaru sama da 8000 da suka wuce ne, 'yan Adam sun fara zama a yankin har ma sun fara samun wayin kansu, kuma a shekaru fiye da 3100 da suka wuce ne, aka kafa birnin.

Ban da haka, Handan ya kuma shahara da wasan Taichi da kuma karin magana, abin da ya sa ake kira shi gari na wasan Taichi da kuma garin karin magana na kasar Sin. Ban da haka, Handan ya kuma shahara da aikin noma, inda ake yawan noman alkama da auduga da masara, har ma ana daukar garin a matsayin rumbun hatsi a arewacin kasar Sin. Har wa yau, Allah ya kuma albarkace Handan da albarkatun kasa, musamman ma tamar karfe da kwal.

A cikin shirin, za a tattauna a kan abubuwan da suka shafi garin na Handan.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China