140627-ziyarar-Maman-ada-zuwa-Handa-1-wasan-Taichi-lubabatu
|
Taichi bai tsaya ga wasa kawai ba, amma wani muhimmin bangare ne na al'adun al'ummar kasar Sin da ke ba da karin haske a kan ainihin al'adun kasar Sin da yadda al'ummar kasashen gabas ke fahimtar abubuwan duniya.
TAIJI ya shafi ilimin gargajiya na kasar Sin, wanda ya hada da "motsi da tsayawa" da kuma "sauri da jinkiri". A ganin Sinawa. "Motsi" yana cikin "tsayawa", "Sauri" yana cikin "jinkiri". TAIJI shi ne jimillar karfinsu.
Fahimtar rayuwa da fahimtar hakikanin abin dake shafar "motsi da tsayawa", don tabbatar da daidaituwa tsakanin zuciya da jiki na mutum da halittu shi ne ma'anar TAIJI.
A wannan mako ne a cikin shirinmu na Allah gari bamban za mu tattauna a kan Taijiquan da aka sani da wasan Taichi, bisa ga ziyararmu a makon jiya zuwa garin Handan da ke lardin Hebei a arewacin kasar Sin, birnin da ya karbi bakuncin dandalin wasan Taichi na kasa da kasa da aka shirya karo na 12 a matsayinsa na mafarin wasan. Sai a biyo mu cikin shirin.