140618-Tasirin-gasar-cin-kofin-kwallon-kafa-na-duniya-ga-tattalin-arzikin-kasar-dake-daukar-bakuncin-gasar-Sanusi.m4a
|
Gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya, gasa ce da kasashe ke fafatawa da juna bayan shekaru hudu-hudu don lashe kofin da hukumar FIFA ta sanya tun bayan da aka kaddamar da gasar a shekarar 1930.
Bayanai sun nuna cewa, an bullo da gasar ce bayan da aka fahimci nasarar da aka samu a wasan kwallon kafa a gasar wasannin Olympics, inda shugaban hukumar FIFA na wancan lokaci Jules Rimet ya fara duba hanyar bullo da wannan gasa baya ga gasar wasannin Olympics.
Bayan cimma daidaito sai aka yanke shawarar fara gasar, inda aka baiwa kasar Uruguay wadda a wancan lokacin take bikin cika shekaru 100 da samun 'yancin kai damar daukar bakuncin gasar a karon farko.
Ya zuwa yanzu an shirya gasar sau 19, inda kasashe daban-daban suka lashe kofin a lokuta daban-daban. Brazil dake daukar bakuncin gasar na shekara ta 2014 wadda za a shafe wata guda ana fafatawa daga ranar 12 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yulin wannan shekara ta lashe kofin sau biyar sannan ita ce kasar dake halartar gasar a kowane lokaci tun da aka fara ta.
Sauran kasashen da suka lashe kofin sun hada da Italiya wadda ta lashe kofin sau 4, kasar Jamus sau 3, Argentina da Uruguay sau biyu-biyu, Ingila da Spaniya sau daya kowane.
Sai dai wani abin takaici shi ne, a shekara ta 1983 an sace kofin da kasar Brazil ta lashe a shekara 1970 kuma har yanzu ba a same shi ba saboda barayin da suka sace kofin sun narkar da shi.
Yanzu dai hukumar FIFA ta tabbatar da cewa, kasar Rasha ce za ta karbi bakuncin gasar ta shekarar 2018, yayin da Qatar za ta karbi bakuncin gasar shekarar 2022, koda yake ana zargin Qatar din ta ba da na goro a kokarin neman daukar bakuncin gasar, zargin da Qatar din ta musanta.
Gasar ta Brazil ta fuskanci bore daga 'yan kasar kan abin da suka kira kashe makuden kudaden shirya gasar da suke cewa bai dace ba. Sai dai masana na cewa, adashe ne da 'yan kasar za su ga fa'idarsa a nan gaba.
Kasashe 32 ne ke halartar gasar ta bana da aka fara amfani da wasu fasahohin zamani, ciki har da tantance shigar kwallo a raga, kuma wasu na ganin cewa, akwai bukatar a kara yawan kasashen zuwa 40 don gwada nasu rabon lashe kofin da yanzu haka yake hannun kasar Spaniya. (Ibrahim/Sanusi Chen)