140611-Matsayin-Masar-bayan-zaben-Al-Sisi-Sanusi.m4a
|
Tun lokacin da sojoji karkashin jagorancin Abdelfatah al-Sisi suka hambarar da gwamnatin Mohammad Morsi bayan zanga-zangar nuna rashin amincewa da gwamnatinsa da wasu daga cikin al'ummar kasar ta Masar suka yi, kasar ta shiga wani hali na rudani, baya ga mutanen da suka rasa rayukansu kana wasu da dama suka jikkata sanadiyar zanga-zangar.
Daga bisani kuma wata kotu a kasar ta haramtawa 'ya'yan jam'iyyar 'yan uwa musulmi (MB) ta Morsi shiga duk wasu harkokin siyasa a kasar ta Masar, matakin da bai yiwa magoya bayan jam'iyyar dadi ba kuma masana ke kallo a matsayin wani makarci na kasashen yammaci da nufin kawo karshen tasirin jam'iyyar baki daya.
Baya ga haramtawa 'ya'yan jam'iyyar ta MB shiga harkokin zabe, an kuma ayyana kungiyar a matsayin kungiyar ta'addanci. Sannan wata kotu har ila a Masar din ta yanke wa wasu magoya bayanta 120 hukuncin daurin shekaru uku-uku a gidan kaso da kuma wasu sama da 600 da aka yanke wa hukuncin kisa a ranar 28 ga watan Faburairu, ciki har da tsohon shugaban jam'iyyar Mohammed Badie bisa zargin nuna karfin tuwo, rura wutar rikici, kone-kone, lalata ofisoshin 'yan sanda da kuma kashe 'yan sanda a yayin zanga-zangar shekarar bara, hukuncin da ya jawo hankalin kasashen duniya.
Masu fashin baki na ganin cewa, dukkan wadannan matakai da sojojin Masar ke dauka a kan magoya bayan jam'iyyar MB, ba zai kawar da tasirinta ba kwata-kwata a Masar. Kuma muddin Al-Sisi yana son ya jagoranci kasar yadda ya kamata, akwai bukatar ya jawo magoyan bayan jam'iyyar ta MB dake son a gina Masar ta yadda za ta dawo da martaba da tasirinta a yankin gabas ta tsakiya, wasu kuma na ganin cewa, idan ya kasa fitar da kasar daga cikin halin da ta shiga, shi ma zai iya fuskantar bore kamar wadanda ya gada. (Ibrahim/Sanusi Chen)