in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar Maman Ada a garin Handan: Ni ma na koyi wasan Taichi
2014-06-14 21:01:48 cri

Hakika kamar yadda na lura, Tai Chi kamar yadda ma'anarta yake wasa ta kiwon lafiya, natsuwa da kuma motsa jiki dalilin da ya sanya wannan wasa take cigaba da samun karbuwa sosai wajen maza da mata, da kuma tsakanin matasa da tsoffi a yawancin kasashen duniya, musammun ma a yankin Asiya, yammacin duniya da ma nahiyar Afrika. Ko shakka babu, ni ma ina daga cikin masu shawar wasan Tai Chi, musammun ma tun wannan zuwana birnin Handan a matsayin yankin mafarin wannan wasa da kuma yadda na samu karin haske kan wannan wasa mai cike da tsawon tarihi, na hadu da malaman Tai Chi da suka shahara sosai a nan kasar Sin musammun ma a nan birnin Handan, kuma wasu daga cikinsu sun yi kokarin koya mini salon wasan Tai Chi ko da yake domin samun kwarewa kan wannan wasan yana bukatar daukar shekaru da dama kafin mutum ya lakance ta sosai, sun koya mini yadda ake lamkwasa hannuwa da yadda kafafu za su tsaya ko kuma yadda mutum zai matso jikinsa cikin armashi tare da sauran sassan jikinsa.

Wannan haduwar kasa da kasa ta wasan Tai Chi ta ba ni muhimmiyar dama ta fahimtarta, ganin cewa a gaskiya a wani lokacin ina tsamanin cewa wasan Tai Chi, wasan fada ne kawai kamar Kungfu da sauransu amma na lura bisa karin hasken wadannan malamai da masana cewa wasan Tai Chi, wasa ne tun fil azal ta samar da lafiyar jiki, natsuwa, zaman jituwa tare da halittun da ke kewaye da mu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China