A cikin 'yan shekarun baya, wasan Taichi ya fara samun karbuwa sosai a kasashen duniya da dama. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yanzu haka akwai mutane fiye da miliyan 150 da ke wasan Taichi a duniya baki daya.
Garin Handan ya kasance wani muhimmin wurin da aka fara samun asalin wasan, don haka ne ake kiransa garin wasan Taichi. Tun daga shekarar 1991, garin na Handan ya fara gudanar da dandalin wasan Taichi na kasa da kasa, dandalin da ke janyo masu sha'awar wasan da kwararrun wasan a kowace shekara. (Lubabatu)