A ranar jiya 13 ga wata ne aka bude gasar wasannin kasa da kasa na Tai Chi karo na goma sha biyu a nan birnin Handan a gaban manyan jami'an birnin Handan da masanan da manyan malaman wasan Tai Chi. Kimanin 'yan wasan Tai chi maza da mata fiye da 1700 da suka fito daga sassa daban daban na kasar Sin da ma wasu kasashe da shiyyoyi 19 sun halarci babbar kwanbala da ta janyo hankalin daruruwan mutane 'yan gari da baki masu sha'awar wasan Tai Chi zuwa kallon wannan gasar dake gudana a wani filin wasannin motsa jiki dake birnin na Handan.
A wannan karo kamar yadda aka saba, gasar ta Tai Chi na gudana zuwa mataki biyu, wato gasar rukuni rukuni da kuma gasar mutum daya daya kuma kamar yadda dokokin wannan wasa suka tanada, kuma alkalai na ba da maki bisa hanyar wasu ka'idoji biyar na wasan Tai Chi.