in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jama'ar wurare daban daban na kasar Brazil sun yi maraba da zuwan wasannin kwallon kafa na cin kofin duniya
2014-06-09 17:13:13 cri

Da raguwar kwanaki 3 masu zuwa da za a shirya wasannin kwallon kafa na cin kofin duniya, ko da yake Barzil take shan wahala da bambancin ra'ayi wajen shirya wasannin, amma tare da kusantowar wasannin cin kofin duniya, jama'ar wurare daban daban na kasar Brazil sun yi maraba da zuwan wasannin.

Mista Ivan Silva shi ne mai gadi na filin wasannin kwallon kafa na Maracana inda za a shirya wasanni zagaye na karshe na cin kofin duniyar, a lokacin dare, Ivan ya yi aiki, a lokacin rana kuma, ya kan sayar da wasu kayayyakin tsaraba na gargajiyar wurin. Ya ce,

"Abubuwan da na sayar da su ne usur, iri na Samba, abubuwan musamman biyu a Rio su ne, samba da kwallon kafa. Ki duba nan, tsuntsu na hummingbird, a Brazil. Za a iya amfani da wannan usur da ake yinsa da itace kamar haka…"

Ban da wurin da ke dab da filin wasanni na Maracana, ya kasance da wasu kayayyakin ado a titunan Rido don maraba da zuwan wasannin cin kofin duniya, a birnin Brasília kuma, jama'a sun fara rataya tutar kasar Brazil a tagoginsu. Wani mai yawon shakatawa a birnin Brasilia mai suna Carlos Alberto ya bayyana cewa,

"Da farkon zuwana a birnin Brasilia, babu ko wani iyali da ya rataya tutar kasa a kan taga. A wata rana, abokina mai suna Jorjao ya rataya tutar kasa a tagar wurin kwana, a rana guda bayan hakan, sai na ga iyalai da dama da ke makwabtaka da shi sun rataya tutocin kasar."

Ko da yake kasar Brazil ba ta gama ginin dukkan filayen wasanni guda 12 na wasannin kwallon kafa na cin kofin duniya ba kawo ya zuwa yanzu, har dai filin wasanni da ke birnin São Paulo, inda za a shirya wasan farko na wannan karo, sau da dama ne aka dakatar da gina shi sakamakon hadari da ya faru yayin gina shi.

Tun asali, kasar Brazil tana burin yin amfani da wasannin cin kofin duniya don inganta manyan ayyukan more rayuwar jama'a na kasar, amma har yanzu akwai ayyuka 30 da ba a gama ginawa ba. Ban da wannan kuma, wani abin da ke sosa rai shi ne, zanga-zangar da jama'ar kasar suka gudanar don nuna adawa ga gwamnatin kasar sabo da kashe kudade masu yawa a wajen shirya wasannin cin kofin duniya na kwallon kafa. Tare da kusantowar wasannin, bi da bi ne a birane da yawa na kasar Brazil, jama'a sun gudanar da zanga-zanga da yajin aiki sakamakon wasannin cin kofin duniya, dukkan wadannan abubuwa sun kawo babbar illa ga wasannin cin kofin duniya na Brazil.

A kasar Brazil, ko da yake wasu jama'a ba su son wasannin cin kofin duniya, a hakika dai yanayin maraba da wasannin ya makara idan aka kwatanta shi da wasanni da aka yi can baya, amma masu sha'awar wasannin kwallon kafa suna ganin cewa, a hakika dai yanzu lokaci bai yi ba tukuna. Ya ce,

"A lokacin wasannin, tabbas ne za a shirya wani gaggarumin biki. Sa'an nan kuma masu yawon shakatawa da suka zo daga kasashen waje za su gamusu da ziyararsu a Brazil sabo da 'yan Brazil suna farin ciki da wannan, kuma zai burge masu yawo. Sa'an nan kuma masu yawo su koma gida cike da farin ciki. A yanzu dai masu yawo baki su kan ga labarai marasa dadi, sun ce ba su jin dadi ba ganin irin wadannan labarai marasa kyau, to, amma sun ce haka abin yake a yawancin kasashe. Amma idan sun zo wurinmu, sun shiga cikin gaggarumin bikinmu, tabbas ne su manta da labarai marasa dadi sabo da a zuciyarsu za su gamsu da abubuwan da za su gain." (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China