in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta dauki matakai da yawa wajen kare muhalli
2014-06-30 10:42:08 cri

Ga wata Hajiya Suwaiba Sulaiman da ta shafe wata guda kawai tana aiki a nan Beijing, ta kan koyi abubuwa daga abokiyarta. Ta ce,

"Akwai wata abokiyar zamana a gidan da nake, sai ko da yaushe ni na cika sanya iska ya shigo mana, sai ta ce, malama ba haka ake yi ba, ta ce, ai idan kika duba ki karanta yanayi na kowace rana ki dinga duba a cikin wuyata ko cikin intanet, ta ce, to, idan kika duba, kika gani babu matsala na gubata yanayi, lokaci ne za ki bude taga, iska ya shigo, amma in iska ba kyau, in ya shigo yana iya haddasa wata matsala ko ciwo. Daga nan sai na dinga amfani da waya in duba in gain, in yanayi yana da kyau in bude taga, inda babu kuma zan bar taga a kulle. Lokacin yarona ya ce, Mami, don Allah ki saya mana abin da ya rufe hancin din, sabo da wannan iska din ya zo. Mu ma muna dauka mataki, domin mu kare kanmu daga gurbata yanayi. Mu ma muna fata ita gwamnatin kasar Sin za ta dauki mataki na magance wannan matsala."

Sabo da kowa da kowa a nan Beijing ya dauki matakai nasa, domin magance gurbacewar iska da kare muhalli. Ban da wannan kuma, kasar Sin ta dauki matakai yawa wajen kare muhalli ciki har da hana bazuwar hamada, da kuma hadin kai da kasashen waje ciki har da Afirka wajen kare muhalli, haka kuma Sin ta samu kyakkyawan sakamako daga kokarin da take yi ciki dogon lokaci wajen kare muhalli. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China