in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matsalar satar bayanan Intanet a tsakanin kasashe
2014-06-05 17:26:26 cri


Tun lokacin da aka fara samun rashin jituwar da ta kai ga fara nuna dan yatsa tsakanin wasu kasashe game da zargin yiwa juna leken asiri, lamarin ya fara shafar huldar dangantaka da sauran batutuwa tsakanin kasashen da lamarin ya shafa.

Lamari na baya-bayan shi ne takun sakar da ta kunno kai game da zargin da Amurka ke yiwa wasu jami'an kasar Sin na yiwa wasu kamfanoninta leken asiri, zargin da Sin ta bayyana a matsayin maras tushe har ma ta dakatar da hadin gwiwar da take yi da Amurka a fannin tsaron yanar gizo.

Ko da yake an sha samun irin wadannan zarge-zarge tsakanin kasashe, amma a kan yi kokarin kai zuciya nesa tare da martaba yarjejeniyar tsaron Intanet din da irin wadannan kasashe suka rattaba hannu a kai don gudun mummunan sakamakon abin da zai biyo baya.

Amma duk da hakurin da wasu kasashe suka nuna na ganin ba su yaye wa juna zane ba, amma lamarin ya wuce abin da ake zato.

Mai kwarmata bayanan nan Edward Snowden ya sheda cewa, Sin tana daya daga cikin kasashen da Amurka ta fi mai da hankali wajen yi musu leken asiri, inda ta yiwa shugabanni, kungiyoyin nazari kimiya da fasahohi, jami'ai da kamfanoninsu leken asiri.

Bugu da kari, Amurka ta kan kai hari kan ma'aikatar cinikayya, harkokin waje, bankuna, kamfanonin sadarwa da jama'a masu zaman kansu, har ma da wasu tsoffin shugabanni da hukumomin gwamnati.

Alkaluma sun nuna cewa, daga ranar 19 ga watan Maris zuwa 18 ga watan Mayu na bana, manyan na'urorin sarrafa bayanai masu kwakwalwa na Amurka da yawansu ya kai 2077 sun shiga na'urori masu kwakwalwa na Sin miliyan 1.18 kai tsaye.

Ban da wannan kuma kwamfutocin Amurka 135 sun sarrafa shafukan Intanet 563 wadanda aka tsara don leken asirin Sin da satar lambobin asirin jama'a, sirrin kasuwa da yin zamba, lamarin da ya kawo babbar hasara ga Sinawa.

Muddin ana bukatar a magance wannan matsala, to kamata ya yi kasashe su martaba yarjejeniyar tsaron intanet da suka rattaba wa hannu, da kuma 'yancin kasashe ba tare da tsoma baki a cikin harkokinsu na cikin gida ba. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China