in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Abubuwan da suka kamata iyaye da suke kwarewa su yi wajen koyar da yaransu
2014-06-03 17:34:18 cri

Iyaye da suka kwarewa kan zama abin koyi a wajen yaransu, kullum suna son su yi ayyuka kamar yadda ya kamata. A yayin da suke kokarin samar wa yaransu kayayyakin da suke bukata na zaman rayuwa da harkokin karatu, a sa'i guda suna kulawa da abubuwan da suke yi. Iyaye da su ka kwarewa su kan yi la'akari da abubuwan da za su taimaka wa girman yaransu, ba su taba nuna shakku kan kwazon yaransu, kuma su kan samar musu dama mai kyau don nuna hazakarsu. Masu sauraro iyaye maza da mata ko kun tabbatar da hakan yayin da kuke koyar da yaranku? A shirinmu na yau, za mu tattauna da ku game da abubuwan da suka kamata iyaye da suke kwarewa su yi wajen koyar da yaransu.

Iyaye maza da mata su ne malaman da suka fi dacewa su koyar da yaransu, ana iya cewa, al'ada marasa kyau da yara suke yi, yawancinsu sun koya ne daga wajen iyayensu. Saboda haka, iyaye da suke da kwarewa su kan mayar da hankali kan al'adar zaman rayuwar yaransu, kamar tashi da wuri daga barci da kuma shiga barci da wuri, tsayawa tsayin daka kan motsa jiki, raba lokaci na kallon talibijin da na karatu yadda ya kamata, kebe al'adar karatu mai kyau, hana yara yin maganganu da furta kalamai marasa kyau, nuna girmama wa ga na gaba, gaida jama'a. Dukkan wadannan abubuwa da muka ambata al'ada ce mai kyau, ana iya cewa, iyaye madubi ne na yaransu, wato ana iya ganin yadda halin iyaye suke ta hanyar duba yadda yaransu suke.

Gaskiya, samar wa yara al'adar zaman rayuwa ta gari na da muhimmanci kwarai. Wannan na taimaka wa wajen koyar da yara darassun zaman rayuwa. To, mene ne iyaye ya kamata su koyar da yaransu a bangaren karatu? Hanyar da ta fi dacewa ita ce, yin karatu tare da yaran.

Ko kana da digirin digirgir ne, kamata ya yi ka rika koya wa yaranka karatu, wannan ba wani aiki ba ne mai wahala, nauyi ne dake kan iyaye. Karanta litattafai tare da yara na taimaka wa yara sosai, hakan na sanya yara su rika daukar iyayensu kamar abokan karatun su. Wannan zai sa yara su yi farin ciki yayin da suke koyo ko samun ilimi, har ma su haddace abin da suka koya cikin sauki. A wannan lokaci, baya ga kasancewa iyaye, ana kuma kara karfafa dangantaka tsakanin iyaye da yaran har ma da kyautata zaman rayuwar yau da kullum.

Ban da yin karatu tare, taimakawa yara wajen kammala aikin da aka ba su a makaranta, shi ma wani abu ne mai muhimmanci sosai. Domin yaran ba za su iya kammala aikin da kansu ba, saboda haka a yayin da suke neman taimako daga wajenku, ya kamata ku dakatar da ayyukan dake gabanku, don taimaka musu su warware matsalar da suke fuskanta. Matakin zai sanya yaranku su ji dadin hadin kai, da kuma fahimtar amfanin hakan

Yayin da yaranku suka gamu da matsaloli, musamman ma a fannin karatu, Me ya kamata mu yi ? Ba shakka kamata ya yi mu fahimci matsalar su kana mu warware ta tare da su. Ga misali, yayin da yaranmu suke bakin ciki saboda ba su samu sakamako mai kyau a jarrabawa ba, a wannan lokaci, bai kamata iyaye mu zarge su ba, a maimakon haka, ya kamata mu taimake su don gano dalilan da suka sa ba su jarrabawar ba, da kuma nazartar abubuwan da suka koyi, kana da kara musu kwarin gwiwa. Fahimtar halin da yara ke ciki da ba su kwarin gwiwa, yana da muhimmanci kwarai ga yara, saboda haka, a duk lokacin da yaranku suka gamu da matsaloli wajen karatu, ya kamata iyaye su yi tunani kan matsalolin, daga baya su warware matsalolin tare da yaran, wannan ne hanyar da ta dace wajen koyar da yara.

To, dazu mun bayyana ayyukan da suka kamata iyaye masu kwarewa su yi wajen koyar da yara. Yanzu, bari mu ci gaba da wannan batu, musamman ma kuskuren da iyaye su kan yi yayin koyar da yara.

Da farko, kada mu tozarta yara a gaban mutane.

Ko da yake yara ba su da girman shekaru, amma wannan ba ya nufin cewa, ba su bukatar girmama wa daga wajen sauran mutane, musamman ma daga wajen iyayensu. Saboda haka, kada mu tozarta yara a gaban mutane, duk da cewa muna da ikon yin haka, amma ba shakka hakan zai zubar musu da mutunci kuma za su ji kunya. A yayin da rayin mu ya baci sakamakon kuskuren da yaranmu suka yi, ya kamata mu yi hakuri, mu kuma yi la'akari da matsayin yaran. Idan ba bu kowa, sai mu gaya musu abin da ya kamata su yi don kada su kara yin kuskure makamancin wannan. Idan iyaye suka iya yin haka, ko shakka babu yaransu za su yi farancin ciki.

Na biyu, bai kamata ba iyaye su rika kiran 'yayansu da wasu kalmomi marasa kyau kamar "wawa", "Mummuna" "Shege" da dai sauransu.

Kafin yaran su balaga, bai kamata iyaye su rika wasu maganganu ba. Idan kullum suna amfani da kalmomi maras kyau kan yaransu, akwai yiwuwar za su yi tsamanin cewa "e, abin da iyayen suke fama a kansa haka haka ne", wannan zai yi illa ga yanayin tashin su.

Na uku, kada iyaye su furta munanan kalmomi ga yaransu.

"Ba na son ka!" "Zan yi wasti da kai idan ka ci gaba da kuka!", irin wadannan munanan kalamai watakila iyaye da yawa sun taba furta wa yaransu. Yayin da mutum ke cikin fushi, ba za su san irin kalaman da ke fita daga bakunansu ba, mu baligai ne kamata ya yi mu fahimci wannan, amma ga yara zai yi wuya su fahimci wannan. Saboda haka, wadannan kalmomi za su bata ran yara kwarai.

Na hudu, kada a yi wa yara hukunci da zarar sun yi kuskure.

Yara su kan yi kuskure, wannan ba abin mamaki ba ne. Bayan da yara suka yi kuskure, abin da ya fi muhimmanci shi ne, iyaye su taimake su wajen gano dalilai don hana abkuwar hakan nan gaba. Yi musu hukunci ba shi ne zai tamaka ga matsalar ba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China