A farkon watan Mayun shekarar bana, wasu malaman koyar da wasan Kungfu na Sin sun kai ziyara a cibiyar al'adun Sin dake Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya, domin yin mu'amala tare da koyar da wasan Kungfu da Taijiquan har na tsawon makwanni biyu. Wannan sh ne karo na farko da aka shigar da wasan Kungfu a kasar Nijeriya tun bayan wannan cibiyar ta kafu a watan Satumban bara, wannan mataki ya taimaka sosai ga wasan Kungfu na Sin wajen samun karbuwa kwarai da gaske a tarayyar Najeriya da ma wasu kasashen Afrika. Wakilinmu Murtala ya tattara labaru kan lamarin, tare da kawo mana wani hoton bidiyo, da fatan za ku ji dadin kallo.