140526-Bin-hanyar-kokarin-raya-ayyuka-a-lokacin-kuruciya-Kande
|
A cikin shirinmu na yau, za a gabatar wa masu sauraronmu wani bayani game da yadda matasa mata suka kokarta don raya ayyukansu. Matasan kasar Sin da aka haife su bayan shekaru 80 na karnin da ya gabata, yawancinsu ba su da 'yan uwa, sai su kadai a cikin gidansu sakamakon tsarin kayyade haihuwa da kasar Sin take aiwatar. Tun suna kanana, iyayensu suke nuna musu kauna da kulawa sosai, ba su taba shan wahalhalu a zaman rayuwarsu ba. Don haka yayin da matasa suka bar iyayensu domin fara raya ayyukansu da kansu, su kan sha wahala sosai.
raya ayyuka ba wata hanya ce ba da ba za'a ci karo da tangarda ba. Tun lokacin da suka taka matakin farko na raya aiki, karancin kudi, gaza yin kasuwanci yadda ya kamata, samu hasarar kudi da dai sauran matsaloli sun dame su sosai. Sun yi bakin ciki, bacin rai, har ma da shiga halin kaka nika yi, amma ba su yi watsi da burinsu ba, bisa kokari ba tare da kasala ba, sun fuskanci kalubaloli iri daban daban, tare da jin dadin lokacin kuruciyarsu.
To, yanzu bari mu shiga labarin Pan Jie, wata Basiniya budurwa.(Kande Gao)