in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shayi na Xinyang na nuna bambancin al'adun shayi na Sin da Afirka
2014-05-27 08:30:11 cri

A wannan makon mun tattauna a kan noman shayi musamman game da bikin baje kolin shayin da aka yi kwanakin baya a birnin Xinyang dake gundumar Henan na nan kasar Sin wanda ya samu halartar wakilan kamfanonin shayi da manoma.

Ganin muhimmancin shayi a tarihin kasar Sin mun duba rayuwan manoman da kuma kokarin kamfanonin sarrafa shayi da shi kan shi yanayin noman shayin da ma nau'in shayin da ake nomawa. Haka kuma mun duba amfanin shayi da yadda kasar Sin take kokarin inganta shi musamman in aka duba tarihin gargajiya da amfanin shi ta bangaren kiwon lafiya wanda nahiyar Afrika za ta iya koyi da wannan dabara na inganta noman albarkatun abinci wadanda za su taimaka ma kiwon lafiya da kara habaka tattalin arzikin kasa da na al'umma.

Mun kuma duba irin nauyin da hukumomi da kamfanoni ke dauka wajen karfafa ma manoma kwarin gwiwwa su iya noma ganyen shayi cikin kwanciyar hankali sannan mun duba barazanar da ke fuskantar sarrafa shayin ta gargajiya dake bukatar amfani da karfin tuwo domin a tabbatar da ingancin shi da dandanon shi na asali wanda matasa ke gujewa saboda aikin dake ciki sun gwammace su yi amfani da injin wanda ba zai ba da cikakken dandanon shayin na asali ba.

Sannan mun kwatanta yanayin shayin mu na gida da ake sha maganin yunwa ko nishadi da na nan kasar Sin da ake sha don lafiyar jiki da kuma al'ada na mutunta bako da daukaka tarihi muka tattauna yadda za'a kara amfana daga bangarorin biyu.

Ganin yadda shugabannin bangarorin biyu wato Sin da Afrika ke kara azama wajen inganta dangantaka ta hanyar samar da fasahohi da horas da jami'ai akwai kuma bukatar musanyar masana a wannan bangaren domin yin nazari a kan noman shayi domin amfanan dukkan bangarori.  (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China