140518-Raayin-iyali-dake-kara-jawo-hankulan-kasa-da-kasa-Bilki
|
Iyali wani muhimmin sashe ne na zaman al'umma, wanda ke taka muhimmiyar rawa wajen harkokin kasa har da na duniya. Ko shakka babu iyali wani bangare ne da ya kamata mu yi kokarin kiyaye shi. Don haka ana iya cewa, zaman alheri na iyali na da nasaba da zaman karko na zaman al'umma.
Ranar 15 ga watan Mayu na shekarar bana, wato ranar Alhamis da ta wuce, ya zama ranar iyali ta duniya karo na 21, inda MDD ta mai da babban taken "Batutuwan da suka shafi iyalai don samun nasarar kudurorin ci gaba" a matsayin ranar iyali ta wannan shekara. A kwanakin baya, an gano wasu tambayoyi a shafunan intanet, saboda wannan ranar iyali ta duniya, ciki har da "Ko ka kan iya tuntubar iyalinka? Yaya ra'ayin matasa yake game da iyali a yanzu? Wadansu abubuwa da suka dauke maka lokaci na tuntubar iyali? "