in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani kyakkyawan kauyen mai suna Haotang na kasar Sin
2014-05-27 08:26:55 cri

Furanni iri daban daban, iskar lokacin bazara ta wuce fuska, muna jin dadi, muna numfashi cikin 'yanci. Da mun wuce wani rafi, sai mu isa kauyen Haotang.

Kauyen Haotang na cikin garin Xinyang na lardin Henan da ke arewacin kasar Sin, kuma kauyen na kewaye da duwatsu. A matsayin wani kauyen dake bada misalin ayyukan samun bunkasuwa cikin dogon lokaci daga cikin kauyukan birnin Xinyang, Haotang ya tsaya tsayin daka kan gina kauyen bisa sigar kyautata hallitu da kare muhalli. Shugabar kauyen Haotang Madam Hu Jing ta ce, za su gina wani aihinin kauye na gaskiya.

"Za mu bi hanyar da muke bi yanzu, mu kara kyautata kauyenmu, don ya zama wani ainihin kauye, ta yadda mutanen birane zasu ji sha'awar zuwa kauyen mu."

Da muke tafiya a kan hanya, mu ga ciyayi da dutse Jigong dukkansu da launin kore. Darektan ofishin da ke kula da harkokin gundumar Wulidian da ke kauye Haotang ke karkashinta, mista Su Yonghua ya gaya mana cewa,

"Wuraren kwana a yankinmu, yawancinsu duk mun yi musu gyara, ba mu lalata su ba, mun kyautata su ne bisa salon musamman na wuraren kwana irin na kudancin lardin Henan. Ku ga wannan gini, wannan dai ana iyar ganin irinsa da yawa a yankunan duwatsu da ke kudancin lardin Henan."

Su Yonghua ya ci gaba da cewa, a kauyen Haotang, a kan yi amfani da rairayi, da tubali, da katako, a yi gyaran wuraren kwana bisa ga hakikanin halin da ko wane iyali ke ciki. An tsara fasali ga ko wane gidan iyali, gwamnati ce ta gayyaci kwararru da su tsara fasalin. Yayin da ake yin gyare-gyare, an fi mai da hankali sosai kan kare muhalin halittu.

"A nan muna kare halittu da muhalli da kyau, manoman wurin sun amince da hanyar da muke bi wajen yin gyare-gyare kan wuraren kwanansu. Ga misali, mu haramta kashe itatuwa don kone su, ta wannan mataki mu kare itatuwa, kuma muna tattara da rarraba shara bisa ga nau'inta. Misalin shara maras leda da roba, mu kan dawo da ita mu sake amfanin da su, wasu shara ana mayar dasu taki, a kauyenmu kowa na da lambun, muna amfani da shara a matsayin taki a cikin lambuna."

Wani muhimmin aiki na kare muhalli shi ne magance matsalar gurbatattun ruwa. Kauyen Haotang yana mai da hankali sosai kan wannan aiki, kowane iyali ya riga ya gama aikin yin gyara kan hanyoyin magance matsalar gurbatattun ruwa. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China