in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da Afrika zai taimaka wajen samun bunkasuwar tattalin arziki da al'umma a duk duniya, in ji masana
2014-05-09 17:35:38 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya yi jawabi a taron kolin Afrika na dandalin tattalin arzikin duniya karo na 24 da aka yi a birnin Abuja, hedkwatar tarayyar Nijeriya, a safiyar 8 ga wata, bisa agogon wurin, inda a cikin jawabinsa, Mr. Li ya jaddada wajibcin kara hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika, tare da sa kaimin bunkasar tattalin arzikin duniya na bai daya, matakinda ya zamanto tamkar samun bunkasuwar tattalin arizki da al'umma baki daya. Jawabinsa ya sami karbuwa sosai daga mahalarta taron kasa da kasa.

A ganin wasu masana, Sin ta baiwa nahiyar Afrika dimbin taimako a wasu fannoni da dama, hakan ya sa ana hasashen cewa, hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu zai samar da dama mai kyau, da kuma raya tattalin arzikin duniya. A cikin jawabin nasa, Mr. Li Keqiang ya nuna cewa, hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika zai kawo moriyar juna, kuma zai baiwa mutane biliyan 2.4 damar cin gajiyarsa, da sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya na bai daya, abin da ya kasance samun bunkasuwar tattalin arzikin da al'umma gaba daya a duniya. Game da jawabin Mr. Li, babbar jami'ar bankin Standard Charter Diana Layfield ta nuna cewa,

"Mr. Li ya tsara wata makoma mai haske ga hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika, wadda a ganina ta zama wata babbar dama mai kyau ga nahiyar Afrika."

Dadin dadawa, kamfanin mai ba da shawara kan shari'a da doka na kasar Birtaniya Mr. David Church ya burge da matsayin da Mr. Li ya bayyana na hadin gwiwa da kasashen Afirka cikin adalci tare da samun moriyar junaya ce

"Sin na dukufa kan baiwa Afirka taimako, Sin ba wai samun moriyarta ita kadai ba a matakan da take dauka, firaministan ya bayyana matsayin da Sin ke dauka na bayar da hakikanin taimako ga kasashen Afrika, abin da ya fi burge mutane da dama."

Tsohon babban jakadan kasar Sin dake Afrika ta kudu, kuma tsohon wakilin gwamnatin kasar Sin kan harkokin Afirka,Mr Liu Guijin ya bayyana cewa, a shekarun baya, Sin ta karkata hanyar da take bi wajen samarwa Afirka taimako, inda ta fara samar wa kasashen Afirka taimako ta hanyoyi daban daban a maimakon gudummawar da ta saba bayarwa a da, matakin da ya nuna cewa, Sin na nacewa ga ka'idar samun bunkasuwar bangarori daban daban, ya ce

"A hakika dai, mun baiwa nahiyar Afrika taimako mai inganci. A shekaru 50 da suka gabata, tsohon firaministan kasar marigayi Zhou Enlai ya kai ziyara Afrika, a wancan lokaci kuma, Sin ta baiwa Afrika taimako gwargwadon karfinta. Amma, taimako a waccan lokaci ya kasance tsakanin gwamnatocinsu kawai. Bayan da Sin ta dauki manufar yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje, musamman ma a lokacin da aka shiga sabon karni, Sin ta fara baiwa Afrika taimako ta hanyoyi daban daban, musamman bisa ga kafuwar dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afrika. Muna fatan ban da samar da taimako gare su, kuma za mu dora muhimmanci kan hadin gwiwa da moriyar juna a fannoni daban-daban, ciki hadda sha'anin noma, Sin ta ba da taimako wajen kafa cibiyoyin koyar da kimiyyar noma fiye da 10, da samar da ayyukan kawar da talauci. A fannin masana'antu kuwa, Sin ta kafa yankuna musamnan na masana'antu shiga a Afrika."

Ban da haka, Mr. Li ya jaddada cewa, abin da aka sa gaba wajen samun bunkasuwar bangarori daban daban shi ne, raya harkokin sufuri. Sin na fatan hadin kai da Afrika wajen shimfida hanyoyin jiragen kasa masu saurin tafiya, hanyoyin motoci masu saurin tafiya da tsarin zirga-zirgar jiragen sama, ta yadda za a sa kaimi ga tuntubar juna tsakanin sassan nahiyar Afirka. Jami'in sashin nazarin harkokin bunkasuwa na asusun raya Afrika Mr. Shi Yongjie ya ganin cewa, Sin da Afrika za su mai da hankali sosai kan wasu ababen more rayuwa nan gaba, ya ce

"A jawabinsa, Li Keqiang ya jaddada muhimmancin kafa ababen more rayuwa, kuma muhimmin matakin da za a dauka wajen raya Afrika shi ne raya masana'antu. Ban da haka, Mr. Li ya gabatar da wani tsarin hadin gwiwa a jawabinsa a hedkwatar AU, na nuna cewa, yawan kudin da Sin za ta zuba wa Afrika kai tsaye kafin shekarar 2020 zai karu zuwa dala biliyan 100 daga dala biliyan 25. Abin da ya nuna cewa, Sin za ta yi hadin kai da nahiyar Afrika ta hanyar zuba jari a fannoni daban-daban."

Dadin dadawa, Mr. Li ya nuna cewa, alkaluman tattalin arzikin Afirka ya kai fiye da dala biliyan 2000, ya zuwa shekarar 2013, 7 daga kasashe goma da suke kan gaba wajen saurin bunkasuwar tattalin arziki kasashe ne na Afrika, abin da ya nuna cewa, Afrika ya zama wani muhimmin ginshiki a wajen raya tattalin arzikin duniya. Mr. Shi Yongjie yana hasashen cewa, kara hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika zai kawo amfani ga Sin da daukacin kasashen Afrika, kuma akwai ma'ana sosai wajen raya tattalin arzikin duniya baki daya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China