140509-ziyarar-Fatimah-a-garin-Xinyang-lubabatu
|
Xinyang Maojian shayi ne da ake noma a garin Xinyang, wanda ya kasance daga daga cikin ganyen shayi guda goma da suka fi shahara a kasar Sin. Musamman bayan da ya samu lambar zinari a gun bikin baje kolin kasa da kasa da aka gudanar a shekarar 1915 a kasar Panama, shayin ya fara yin suna har a duniya baki daya.
Xinyang birni ne da ke kudancin lardin Henan na kasar Sin, wuri ne mai matukar ni'ima. Kwanan nan, wakiliyarmu Fatimah Jibril ta kai ziyara birnin, sai a bi sawunta cikin shirin, domin samun karin haske a kan garin da kuma shayin da yake fitarwa.(Lubabatu)