in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin shimfida hanyoyi da gadoji na kasar Sin ya kawo babban tasiri ga ci gaban kasar Angola
2014-05-09 16:41:46 cri

Bayan da aka kaddamar da dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a shekara ta 2000, ba ma kawai kamfanonin Sin sun taimaka wa kasashen Afirka kan muhimman ayyukan more rayuwar jama'a, hadin kan tattalin arziki da cinikayya, har ma suna dora muhimmanci kan horar da kwararru domin kara karfin kasashen Afirka wajen samun ci gaba. Kamar yadda Sinawa su kan ce, ya fi kyau a koya wa mutane kamun kifi a maimakon ba shi su kifi kullum. Abokiyar aikin mu Kande ta hada ma rahoton kan yadda kamfanin shimfida hanyoyi da gadoji na kasar Sin ya kawo babban tasiri ga ci gaban kasar Angola.

Masu sauraro, wakar da kuke saurara wata waka ce mai taken "Furen Jasmine", wadda dalibai 'yan asalin kasar Angola 31 da suka taba zuwa kasar Sin neman ilmi suka rera. Wannan waka ta burge Du Fei, mataimakin babban manaja na kamfanin shimfida hanyoyi da gadoji na kasar Sin kwarai da gaske. Yau da shekaru biyu da suka gabata, wadannan dalibai da kamfanin ya dauki nauyin biyan kudin karatunsu wajen koyon ilmin gine-gine a jami'ar ilmin kimiyya da aikin injiniyoyi ta Changsha sun taba rera wannan waka a gun bikin kammala karatunsu, domin bayyana wa kamfanin da kuma jami'ar sahihiyar godiyarsu. A matsayinsu na 'yan kasar Angola dake cikin rukunin farko na shirin horar da kwararru da kamfanin shimfida hanyoyi da gadoji na kasar Sin da ma'aikatar tsara birane da gine-gine ta Angola suka gabatar cikin hadin gwiwa, yanzu dai wadannan dalibai sun riga sun zama manyan kusoshi wajen raya kasarsu. Yayin da Du Fei ya tuna da halin da kamfanin ya je kasar Angola, ya ce,

"A shekara ta 2004 ne, kamfanin shimfida hanyoyi da gadoji na kasar Sin ya fara aikinsa a kasar Angola. Ganin cewa kasar ta kawo karshen yakin basasa ba da jimawa ba, da kuma karancin kayayyakin gine-gine da ma'aikata, mun tsai da kudurin horar da wasu mutanen 'kasar da ke rike da fasaha. "

A yayin taron ministoci karo na uku na babban taron dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka da aka shirya a shekara ta 2006, Hu Jintao, shugaban kasar Sin a wancan lokaci ya gabatar da shirin horar da kwararru daga Afirka 15000 a cikin shekaru uku masu zuwa. Sabo da haka, kamfanin shimfida hanyoyi da gadoji na kasar Sin ya hada kai tare da ma'aikatar tsara birane da gine-gine ta Angola wajen horar da kwararru 'yan asalin kasar Angola da za su taimaka wa kasarsu. Dalilin da ya sa aka kaddamar da shirin horaswa da muka yi magana a baya. A shekara ta 2007, daliban kasar Angola 31 sun shiga jami'ar ilmin kimiyya da aikin injiniyoyi ta Changsha don koyon ilmin shimfida hanyoyi da gadoji. Kuma kamfanin ya biya kudin karatunsu baki daya, kudin da suka biya ya zarce dalar Amurka miliyan uku gaba daya.

A tsawon shekaru biyar, ba ma kawai wadannan dalibai sun koyi Sinanci da fasahohi ba, har ma sun kulla dankon zumunci tare da abokansu Sinawa, har ma sun dauki kasar Sin a matsayin wata kasarsu ta daban. Lotes Sabino, daya daga cikin daliban ya furta cewa,

"Tabbas ne zan koma kasar Sin don ziyara, sabo da ina da abokan arziki da yawa a can, wadanda su 'yan uwanmu ne, kasar Sin kuma ta kasance tamkar garinmu ne."

Bayan da wadannan dalibai suka kammala karatu suka koma gida, dalibai fiye da 10 sun samu damar shiga kamfanin shimfida hanyoyi da gadoji na kasar Sin, wasu kuma sun shiga ma'aikatar tsara birane da gine-gine ta Angola. Jose Joanes Andre, mataimakin shugaban ma'aikatar ya darajanta matakan horar da kwararru da kamfanin kasar Sin ya sa hannu a ciki. Yana mai cewa,

"ko da yaushe kasar Sin kasa ce da ta kan nuna goyon baya sosai ga Angola wajen horar da kwararru. Idan babu kwararru to babu ci gaban kasa, don haka muna fatan ci gaba da hadin kai tare da kasar Sin a wannan fanni. Haka kuma muna alfahari da yadda kamfanin shimfida hanyoyi da gadoji na kasar Sin ya horar da kwararru ga Angola."

A cikin shekaru goma da suka gabata bayan da kamfanin ya shiga kasar Angola, ya sa hannu cikin muhimman ayyukan more rayuwar jama'a na kasar fiye da 40, kuma ya samar da guraban aikin yi fiye da dubu 20 ga 'yan kasar. A cikin manyan ayyukan yau da kullum guda 7 da ake gudanarwa, ana iya samun ma'aikata 'yan kasar 1762, wadanda yawansu ya kai kusan kashi 67 cikin dari bisa jimillar ma'aikatan da suke aiki a kamfanin.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China