in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar da firaministan kasar Sin ya yi a Najeriya ta ciyar da hadin kai tsakanin kasashen biyu gaba
2014-05-08 15:07:28 cri

A safiyar jiya Laraba, firaministan kasar Sin Li Keqiang wanda a yanzu haka ke ziyarar aiki a kasar Najeriya, ya yi ganawa da shugaba Goodluck Jonathan a birnin Abuja, inda suka amince da zurfafa hadin kai a tsakanin kasashensu a fannonin manyan kayayyakin more rayuwar jama'a, sha'anin noma, makamashi, zirga-zirgar jiragen sama da dai sauransu, sannan daga baya suka halarci bikin daddale wasu yarjejeniyoyi tsakanin kasashen biyu.

Firaminista Li na gudanar da wannan ziyara ce lokacin da Najeriya ke fuskantar barazanar tsaro bayan aukuwar jerin farmakin ta'addanci da aka kai a kasar ba da dadewa ba. Saboda haka, shugaba Jonathan ya yaba ma ziyarar da firaminista Li ya kai wa kasar kamar yadda aka tsara.

"Sakamakon yanayin tsaro mai tsanani da kasar Najeriya ke ciki, babu wanda ke son ziyartar kasar, firaminista Li ya iso kasarmu ne bisa shirin da muka tsara, wannan na nuna goyon baya sosai da yake yi wa Najeriya. Muna yi godiya kwarai da ainihin zumunci da firaminista Li ya nuna mana."

A yayin shawarwarin da aka yi a wannan rana, firaminista Li ya bayyana cewa, kasar Sin ita ce kasar da ta fi girma wajen samun saurin bunkasuwar tattalin arziki a yankin Asiya, Najeriya ma na rike da wannan matsayin a nahiyar Afrika, sannan kuma dukkansu kasashe ne masu yawan mutane. Saboda haka, karfafa hadin kai a tsakanin kasashen biyu na da amfani wajen samar da alheri ga jama'arsu, har ma zai taka rawa wajen samun bunkasuwa da wadata a yankunansu da ma duk duniya baki daya. Ya ce,

"Hadin kai a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da al'adu, tushe ne na batun hadin kai tsakanin kasashen Sin da Najeriya, shi ne kuma muhimmin batu da zan inganta a wannan ziyarar. Muna son gudanar da hadin kai a fannonin da suka shafi manyan kayayyakin more rayuwa, kudi, zuba jari, raya kayayyakin amfanin gona, ayyukan zirga-zirgar jiragen sama da sararin samaniya, da dai sauransu."

Firaminista Li ya kara da cewa, manyan jiragen sama masu cin gajeren zango da kamfanonin kasar Sin suka nazarta da kansu, ba kawai suna da inganci sosai ba, har ma farashinsu ya kai matsayin yadda ya kamata, saboda haka, sun dace da kasuwar Afrika kwarai. Kasar Sin na fatan kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na kasashen Afrika, ciki har da Najeriya za su mai da su a matsayin gaba wajen zaben jiragen sama da suke bukata. Game da hakan, shugaba Jonathan ya bayyana cewa, kasar Najeriya na maraba da kamfanonin Sin da su kara zuba jari a cikin ta, sannan ita ma za ta samar da muhalli mai kyau wajen zuba jarin.

Bayan haka kuma, Shugaba Jonathan ya kara jaddada fatansa na shigar da kamfanonin Sin cikin ayyukan gina hanyoyin dogo dake bakin teku a Najeriya, abin da ya sa firaminista Li ya mayar da martani mai yakini kan wannan bukata. Ya ce,

"Gwamnatin kasar Najeriya da jama'arta suna mayar da hankali sosai kan gina hanyoyin dogo dake bakin teku, wasu kamfanonin Sin suna sha'awa sosai kan wannan batu, don haka gwamnatin Sin za ta inganta aikin tattara kudi, da sauran ayyukan hadin kai da abin da ya kamata. Bangarorin biyu za su yi kokari tare don soma ayyukan na gina hanyoyin dogo dake bakin teku cikin lokaci, domin samar da alheri ga jama'ar Najeriya, ta hakan ne za a iya tabbatar da samun nasara tare tsakanin kasashen Sin da Najeriya."

Haka zalika, shugaba Jonathan ya ce, shekara mai zuwa shekara ce ta cikon shekaru 10 da aka kulla huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen Najeriya da Sin, a dalilin haka ne Najeriya take son kokari tare da kasar Sin wajen amfani da wannan dama mai kyau don ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi. Ban da wannan kuma, Najeriya ta yi godiya ga Sin saboda taimako da goyon baya da ta ba ta, da nahiyar Afrika, da kuma kungiyar ECOWAS a cikin dogon lokaci. A ganin shugaba Jonathan, shirin hadin kai tsakanin kasashen Afrika da Sin da firaminista Li ya gabatar a cikin jawabinsa a cibiyar kungiyar AU, zai amfanawa ci gaban nahiyar Afrika. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China