in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dangantaka tsakanin Sin da Afrika za ta cigaban juna
2014-05-08 12:06:42 cri

Sin da kasashen Afrika za su yi iyakacin kokarinsu na inganta hadin gwiwwa a bangaren tattalin arziki wanda zai karfafa shi ya kawo cigaba a bangarorin biyu, har ma da farfado da bangaren ta fuskar kasashen duniya baki daya.

Masana'antu, hada-hadar kudi, rage talauci, kare yankuna daga zaizayar kasa, musanyar al'adu, zaman lafiya da tsaro, duk suna cikin abubuwan da firaminista Li zai jaddada a kan su lokacin ziyarar shi a Afrika. Za'a kuma samar da karin taimako a bangaren zuba jari, ba da rance, samar da ababen more rayuwa da sauran taimako na kudi, duk a sabon tsarin inganta zumunci tsakanin sassan biyu.

Huo Jianguo, darekta a makarantar ciniki na kasashen waje da hadin gwiwwa na tattalin arziki a kasar Sin ya ce, bangarorin biyu sun kasance a matsayi daya na cigaba a cikin shekaru 5 a jeer, tare da samun habakar tattalin arziki, duk da rikicin tattalin arzikin duniya da aka fuskanta.

A shekara ta 2013, ciniki tsakanin bangarorin biyu ya kai dalar Amurka biliyan 210.3 bayan a shekarar ta 1965, wannan matsayi na kimanin dalar Amurka miliyan 250 kawai, abin da ya sa Sin ta zama babbar abokiyar ciniki a nahiyar Afirka a cikin shekaru 5 a jere. Ta zuba jari kai tsayi na sama da dalar Amurka biliyan 25 a Afrika, ya zuwa karshen shekarar bara kuma, fiye da ma'aikatu 2,500 suna kasuwancinsu a wannan nahiyar a bangarori daban daban.

Hadin kai a bangaren tattalin arziki da ciniki yana taka muhimmiyar rawa wajen zurfafa zumunci tsakanin Sin da nahiya Afrika, in ji Liu Hongwu na cibiyar karatun nahiyar Afrika dake jami'ar horar da malamai ta Zhejiang. Ayyukan hadin gwiwwa a Afrika sun inganta tattalin arzikin wadannan kasashe, sun kuma samar da ayyukan yi, tare da ingiza samar da masana'antu.

Ministan kasuwanci na Sin Gao Hucheng yana fatan samun hadin gwiwwa mai zurfi da zai kara shigar da Sin a nahiyar, tare da inganta dangantaka tsakanin bangarorin biyu. Fatan da ya zo daya da na Zhou Yongsheng, shaihun malami a jami'ar harkokin kasashen wajen Sin, wanda ya ce, ayyukan hadin gwiwwa tsakanin Sin da Afrika sun nuna alamun cigaba, ganin yadda bangarorin biyu suke ta himmatuwa wajen amfana daga junansu.

Nahiyar Afrika dake da al'umma biliyan daya, sannan take da GDP na dalar Amurka fiye da triliyan 2 ta samu cigaban tattalin arziki na sama da kashi 5 a cikin 100 a duk shekarar cikin shekaru 10 a jere, sannan bugu da kari a cikin kasashe da suka fi samun saurin cigaban tattalin arziki a duniya 6 daga cikin kasashen 10 sun fito daga Afrika. Sai dai a ra'ayin Huo Jianguo, habaka dangantaka tsakanin Sin da Afrika zai hada da zuba jari cikin hadin gwiwwa, da samar da taimakon kudi ta hanyar da kowane bangare zai amfana da juna.

A mataki na gaba kuma na kasuwanci cikin hadin gwiwwa da ya fi musanyar kayayyaki masarufi da albarkatun gona zai taimaki Afrika ta inganta hanyoyin sarrafawa tare da kerawa, wadda ta hakan zai shawo kan matsalar dogaro da ake yi a kan kayayyakin da aka shigo da su daga kasashen waje.

Ma'aikatun kasar Sin za su iya gina karin masana'antu tare da mazauna wadannan kasashe domin taimakawa samar da ababen bukata na gida da masaku, tufafi da sauran abubuwan amfanin yau da kullum a cikin gida, ba sai an fita waje ba. Inganta hadin gwiwwa tsakanin Sin da Afrika duk da alfanun da yake da shi ma ita kanta Afrika ta kuma tafi daidai da tsarin tattalin arziki da Sin ta fitar a cikin gida.

Mr. Liu Guijin, darekta a makarantar kasuwanci tsakanin Sin da afrika a karshin jami'ar horar da malamai ta Zhejiang ya ce, hadin gwiwwar zai ba da dama ga Sin, ta mika wassu dabaru na masana'antu ga Afrika wadda za ta habaka kwaskwarima a wannan fanni a kasashen. Har ila yau hadin gwiwwa ta hada-hadar kudi, duk da zai cimma bukatun Afrika zai kuma karfafa kudin kasar Sin Renminbi.

Kasar Sin ta yi alkawarin kara adadin bashin da za ta baiwa kasashen Afrika da dalar Amurka biliyan 10, adadin da yanzu ya kai biliyan 30. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China