140507-Kasashen-Sin-da-Afirka-suna-yin-hadin-gwiwa-irin-ta-a-zo-a-gani-Sanusi
|
A ranar Lahadi 4 ga wata ne firaministan kasar Sin Li Keqiang ya fara wata ziyarar aiki ta kwanaki hudu a kasashe hudu na Afirka ziyarar da masana ke bayyana wa a matsayin wani muhimmin aiki diflomasiya da ya shafi fadin nahiyar Afirka.
Ziyarar Mr Li zuwa kasashen Afirka a wannan karo wadanda suka hada da Angola, Kenya, Najeriya da Habasha, ita ce ta farko a nahiyar tun bayan da ya zama firaministan kasar Sin, kana ziyararsa ta biyu a nahiyar ta Afirka.
Firaministan na Sin ya zabi Angola ne saboda tana daya daga cikin kasashen Afirka da suke samun ci gaba cikin sauri a 'yan shekarun nan, sai Kenya wadda ta kasance kasa daya tak da ke da ofishin shirin lura da muhalli na MDD ko UNEP.
Sannan an zabi Habasha ne saboda kasancewar hedkwatar AU a wurin, wannan ya sa ake daukar Addis Abba a matsayin hedkwatar siyasa da diflomasiya ta nahiyar Afirka, yayin da ita kuma Najeriya ta kasance kasar da ke kan gaba wajen yawan al'umma a nahiyar kana kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar ta Afirka baki daya.
Sai dai jawabin da Li Keqiang ya yi a hedkwatar AU ta sosa ran nahiyar, ganin yadda ya tabo wasu muhimman sassan da ke yiwa nahiyar kaikayi tare da jaddada aniyar kasar Sin na taimaka wa nahiyar.
Firaminista Li Keqiang ya bayyana nahiyar ta Afirka da cewa, tana daya daga cikin ginshikan duniya a fannin tattalin arziki, wayewar kai, tarihi, al'adu. Sannan ya ce, idan har Sin da Afirka suka samu ci gaba tare, duniya za ta kyautata.
Bugu da kari, firaministan ya bayyana burin kasar Sin na tallafawa sojojin kiyaye zaman lafiya na Afirka da fasahohi, samar da kayayyakin more rayuwar jama'a, raya birane, inganta aikin gona, kare muhalli, kwararowar Hamada da sauransu.
Sauran sun hada da sabunta salon yin hadin gwiwar Sin da afirka ta yadda zai dace da yanayin da duniya ke ciki, yaki da ayyukan ta'addanci, kara hada kai da amincewa da juna, girmama juna, moriya tare da neman bunkasuwa cikin hakuri.
Jawabin na Mr Li a cewar masu fashin baki, ya nuna niyar kasar Sin na taimaka nahiyar ta Afirka ta yadda za a gudu tare a tsira tare. (Ibrahim yaya, Sanusi Chen)