in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Huawei na kasar Sin ta horas da mata dubu daya na kasar Nijeriya
2014-05-07 14:44:41 cri


A kokarin kara zurfafa dangantaka a tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannoni daban daban, ban da ayyukan more rayuwar jama'a, kamfanonin kasar Sin sun kara zuba jari kan sauran fannoni, ta yadda za su iya samar da moriya ga zamantakewar al'umma a hanyoyi daban daban. A matsayin kamfanin kasar Sin na farko da ya kafa cibiyar horaswa a kasar Nijeriya, kamfanin Huawei ya horas da mata dubu daya kasar fasahohin sadarwa.

Game da burin kamfanin Huawei na kafa cibiyar horas da matan Nijeriya, shugaban da ke kula da harkokin wannan aikin horaswa, kuma manajan da ke kula da harkokin horo da ciniki a yankin yammacin Afirka na kamfanin Huawei Mista Li Jinxing ya bayyana cewa,

"Har kullum samun aikin yi ga wassu jama'ar Nijeriya baya da sauki musamman ma mata wadanda suke wahala sosai wajen samun ayyukan yi. Ministar sadarwa ta Nijeriya mace ce, wadda take mai da hankali kan samar da ayyukan yi ga mata, sabo da haka ne kamfanin Huawei ya jagoranci wannan aiki, domin gudanar da wannan horas tare."

Bisa hadin gwiwar Huawei da ma'aikatar sadarwa ta Nijeriya, an kadammar da wannan aikin horaswar a hukunce a watan Nuwamba na shekarar 2013 a birnin Lagos, a Nijeriya, kuma bisa shirin da aka tsara, za a horas da mata dubu a zangon farko.

Game da sakamakon da aka samu daga wannan aikin horaswar, wadanda suka samu wannan horo za su samu ilimi a wannan bangaren. Veronica Ezekiel da ta fito daga jihar Taraba da ke Arewa maso gabashin Nijeriya, ta taba koyon manhajan kumfuna, amma ba ta san fasahohin bayanai da sadarwa ba. Bayan da aka shafe kwanaki da dama ana horas da ita, yanzu ta samu karin ilimi a cikin wannan fannin da ba ta taba shiga ba a da.

"Abin da ake koya mana yanzu yana nan kaman abin da muke yi ko wane rana ne, ba ma gane wa sabo da ba mu san abin da yake faruwa ba, amma yanzu yadda ake koyo mana da yadda mu muke samu muke ko wanen rana kowa yana ganewa kuma yana da kyau sosai. Malaman ma suna nan da kayatarda kuma suna nan da ganewa sosai kuma suna yi shi daidai da yadda mu za mu gane sosai."

A matsayin bangaren da ke hadin kai da Huawei wajen shirya aikin horas, wani jami'in ma'aikatar sadarwa ta Nijeriya Jude Akpan ya shiga darusan da dama a 'yan kwanakin baya. Kwarewar da malaman Huawei suke da ita, da abubuwa masu amfani da suke koyar da dalibai, da kaunar da mata ke da shi wajen koyon ilmi, dukkansu sun sanya Jude Akpan zama cike da imani ga makomar bunkasuwar matan nan.

"Sanin kowa ne cewa, maza ke rike da matsayin ginshiki a fannin fasahohin bayanai da sadarwa. Na yi imani cewa, aikin horawar da muke gudanar wa a yanzu zai koyar da mata fasahohin sadarwa, don su samu fiffiko wajen fasahohi, bayan da suka gama karatu kuma, za su iya samun damar kirkire-kirkire, ban da wannan za su shiga cikin kamfanoni. Game da mata da ke son raya sana'o'insu a fannin fasahohin bayanai da sadarwa, aikin horon ya kasance wata kyakkyawar dama gare su."

Mista Jude Akpan ya ci gaba da cewa, ma'aikatar sanarwa ta Nijeriya za ta mayar da shirin horas da mata dubu daya a matsayin wani muhimmin dandali, wanda za ta iya amfani da shi wajen habaka hadin kai da kamfanin Huawei, musamman a fannonin ayyukan manhaja, da ayyukan shafunan intanet, da ayyukan bayanai da dai sauransu, ta yadda za a iya kara samar wa jama'ar Nijeriya moriya.

Shugaban da ke kula da harkokin yammacin Afirka na kamfanin Huawei Mista Peng Song ya bayyana a bikin kaddamar da aikin horas din cewa, Huawei ya shafe shekaru 14 yana bunkasuwa a yammacin Afirka, Huawei ya dauki matakai da yawa ciki har da shigar da ma'aikatan Nijeriya a cikin kamfani, da habaka zuba jari a Nijeriya, da sa kaimi ga samar da ayyukan yi ga jama'ar Nijeriya, don more nasarorin kasuwanci da Nijeriya da jin dadin jama'ar wurin, wannan dai ya samu amincewa daga fannoni daban daban na Nijeriya. Ban da kamfanin Huawei, kamfanonin kasar Sin masu yawan gaske sun mai da hankali kan inganta kwarewar jama'a da kara samar da ayyukan yi ga jama'ar Nijeriya. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China