in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'ar Peking ta gudanar da taron karawa juna sani game da Al'adu da Adabin Afirka
2014-05-05 17:43:03 cri

Sashen nazarin yaruka da adabin nahiyar Asiya da Afirka, da hadin gwiwar cibiyar nazarin harkokin nahiyar Afirka na jami'ar Peking dake nan birnin Beijing, sun gudanar da wani babban taron karawa juna sani, game da nazarin yaruka da Adabin nahiyar Afirka.  

An dai sadaukar da wannan taro wanda shi ne irin sa na farko ga marigayi Farfesa Chinua Achebe, shahararren marubucin adabin nan dan Najeriya da ya rasu a bara. Forfesa Wei Liming, darektar sashen nazarin harsunan Asiya da Afirka a kwalejin koyar da harsunan waje na jami'ar Peking ta ce, domin tunawa da cika shekara daya da rasuwar marigayi Chinua Achebe, za a gudanar da bukukuwa da dama a wannan shekara a duk fadin duniya, kuma jami'ar Peking a nata bangare tana son yin amfani da wannan dama, domin a yi nazartari kan halin da ake ciki a kasar Sin, ta fannin aikin koyar da harsunan Afirka, da ma adabin kasashen nahiyar, ta yadda za a kara inganta wannan aiki. Ta ce, "Jami'ar Peking na daya daga cikin fitattun jami'o'in kasar Sin, wadda kuma take kan gaba a kasar Sin ta bangaren nazarin harkokin Afirka, sai dai nazarin da ake yi a duk fadin kasar kan harkokin Afirka da ke kudu da Sahara bai isa ba . A jami'ar Peking, akwai malamai daga sassa daban daban da ke gudanar da ayyukan nazarin adabin Afirka, don haka, muna so mu tara su wuri daya, don mu mai da hankali a kan adabin Afirka da ma yin nazari a kai tare."

Taron da ya gudana a ranar Juma'ar da ta gabata, wanda kuma aka yiwa lakabin "Koyarwa da bincike kan yaruka da Adabin nahiyar Afirka" ya samu halartar masana da dama daga kasashen Afirka, da takwarorin su dake nan kasar Sin.

A jawabinsa na fatan alheri, mukaddashin jakadan Nigeria a nan kasar Sin Shola Onadipe, godiya ta musamman ya yi ga mashirya, tare da daukacin bakin da suka samu halartar taron. Ya na mai jaddada muhimmancin sa, musamman a wannan lokaci da kasar Sin, da takwarorin ta na Afirka ke dada kaimin bunkasa musayar al'adu tsakanin su.

Cikin jawabin da wakilinsa Godwin Ifeanyi Okoro ya karanta, Ambasada Onadipe ya bayyana taron, a matsayin wata kyakkyawar hanyar yayata gudummawar da farfesa Achebe ya bayar, ga ci gaban al'adu, da akidun al'ummar Afirka ga kasashen waje.

Da yake gabatar da jawabinsa na maraba, daya daga kwararrun malamai a fannin nazarin yaruka da adabin Afirka, wanda shi ne tsohon darektan sashen nazarin wasannin kwaikwayo a jami'ar Ibadan, kuma malami a jami'ar ta Peking Farfesa Femi Osafisan, bayyana taron na wannan karo yayi, a matsayin wani ginshiki na kara habaka dangantakar dake tsakanin Sin da Nigeria, da ma nahiyar Afirka baki daya, musamman a wannan fage na bincike da musayar ilimin adabi da nazarin yarukan sassan biyu.

Jim kadan da kammala zaman taron, mun samu zantawa da farfesa Osofisan, wanda ya yi karin haske game da muhimmancin da wannan taro ke da shi. "Dama dai tuni muke ta habaka sassa daban daban na hadin gwiwa, ciki hadda cinikayya da kasuwanci da sauransu, amma fannin al'adu shine ke baiwa sassa damar sanin junan su. Musa Muna fatan sanin Sinawa, kuma Sinawa ma na burin fahimtar mu. Ta wannan hanya ta musayar al'adu ne hakan zai kasance. Domin ba fa'ida ace kana cinikayya da mutanen da ba ma ka sansu ba. Kuma abin takaici ne saboda tarihimmu mun fi sanin al'umuun ummun yammacin duniya, kusan bamu san wani abu mai yawa daga al'ummar Asiya ba. Amma ta hanyar Adabi, kamar yadda rubutun Farfesa Achebe suka yi tasiri, abu ne mai sauki masu tasowa su fahimci abinda yake na hakika a kasashen na mu."

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China